Hanyoyin dakile ta’addanci

Ayyukan ta’addanci al’amura ne da duniya ta saba ji da gani, amma ba su taba yaduwa a kasashe masu yawa kamar yadda suka yadu a cikin ’yan shekarun da suka gabata ba. A baya dai ayyukan ta’addanci sun takaitu ne a wasu yankuna, ko kasashen duniya, amma bayan  bayyanar kungiyoyin ’yan ta’adda irinsu Alka’ida da […]

Hanyoyin dakile ta’addanci
Hanyoyin dakile ta’addanci

Ayyukan ta’addanci al’amura ne da duniya ta saba ji da gani, amma ba su taba yaduwa a kasashe masu yawa kamar yadda suka yadu a cikin ’yan shekarun da suka gabata ba. A baya dai ayyukan ta’addanci sun takaitu ne a wasu yankuna, ko kasashen duniya, amma bayan  bayyanar kungiyoyin ’yan ta’adda irinsu Alka’ida da al-Shabab da Boko Haram da sauransu.
daruruwan matasa daga kasashen Turai da Nahiyar Afirka da Amurka sun shiga wadannan kungiyoyi, ta yadda bangare mafi yawa na mayakan kungiyoyin, wadanda suke yaki da gwamnatocin kasashen Siriya da Najeriya da Somaliya da Iraki sun fito ne daga kasashen waje.
Kawo zuwa yau akwai wasu dalilai wadanda suke taimaka wa ayyukan ta’addanci suke son mamaye duniya da farko akwai matasan da suka shiga wadannan kungiyoyi da sunan taimaka wa addinin Musulunci, wanda muna iya cewa jahilcin addinin ne ya kai su ga fadawa cikin tarkon wadannan kungiyoyi da kuma gazawar da malaman addinin suke yi na isar da sakon Musulunci na gaskiya ga wadannan matasa, wadanda suke son sanin addinin.
Sai kuma yada gurbatattun akidun Musulunci ga matasa wadanda ba su taba sanin addinin Musulunci ba, wanda masu akidar banza suke yi, musamman a kasashen Turai da Amurka. Sai kuma wani dalili mai muhimmanci, wanda muna iya cewa, ya dara sauran muhimmanci, wato kudi masu yawa, wadanda ’ya’yan wadannan kungiyoyi suke samu a lokacin da suka mamaye wasu yankuna, musamman a Nahiyar Afirka da talauci ya yi mana katutu, wannan ya taimaka wa ’yan ta’addar samun matasa marasa aikin yi a duk fadin duniya, inda suka yi ta daukarsu aiki da horar da su kan ayyukan ta’addanci.
Ina ganin ya kamata a ce gwamnatin Najeriya ta hada gwiwa da malaman addini, wajen daidaita lamuran matasa. Tabbas na sani kuma kowa ma ya sani cewar, ’yan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa da addu’o’in duk don neman biyan bukata, kuma Allah Ya biya bukatarmu, canjin da aka jima ana nema ya zo. Bisa al’ada idan ka yi addu’a har ka samu biyan bukata, ya zama dole ka yi wa wanda Ya ba ka nasarar godiya, ma’ana ka gode wa Allah da Ya amsa maka addu’ar. Amma muddin mutum ya yi butulci, hakika za ka iya samun kanka cikin wata matsalar daban. Talakawan Najeriya sun ci nasara, sun juya akalar shugabancin kasar da hannayensu, sun kuma mika al’ammarinsu a hannun amintattun shugabannin da suka zaba.
Kamar yadda hasashen Gwamnatin Najeriya ya nuna cewa akwai matasa masu yawo ba sa komai, sama da miliyan 12, idan kuwa haka ne duk kasar da ba ta kula da wannan ba, nan gaba za a iya samun matsala. Shi ya sa nake ganin ya kamata gwamnati ta hada kai da malaman wajen samar wa daliban sana’a, ta hanyar da ya kamata; kuma a yi kokarin ganin suna karatu; kuma suna da abin yi, ina ganin hakan zai rage shiga kungiyoyi irin na ta’addanci. Misali za ka ga samari suna shaye-shaye ga zaman banza wasu sun gama karatu babu abin yi, wadannan wace harkar kudi ce za ta zo musu komai muninta ba su shiga ba? Gaskiya ya kamata gwamnati ta duba.
Kuma a cikin wani Hadisin Annabi (SAW) ya ce: “Mutukar al’umma suna yin zina ko luwadi da madigo, Allah zai saukar  musu da annobar mutuwa da fari, kamar yadda ake ciki a yanzu.” Kowa yana ganin irin halin da muke ciki, haka a fadin duniya kazanta ta yi yawa, kuma ba fa zabar  Buhari ne kawai zai canja halin da muke ciki ba, matukar galibin jama’a ba su gyara halinsu ba, sun tsarkake zukatansu tsakani da Allah ba, tilas ne kowanenmu ya daura aniyar fara gyara daga kansa. Allah Ya kare mu, amin.
Don haka dole ne su ma shugabannin kasashen duniya su yi sauri, wajen tumbuke cibiyoyin wadannan kungiyoyi daga asalinsu, ta hanyar toshe dukkan hanyoyin da suke samun kudi da kuma taimako don ganin musifar ba ta kara game duniya ba.
Anas Saminu Ja’en, Gidan Makera Ja’en Kano, 07033882307.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno