Hanyoyin dawo da kishin kasa
Dasa kishin kasa a zukatan ‘yan kasa yana sa kishin kasa, kuma hakan yana daya daga cikin dalilan da suke sa wa a tarar da mutane suna kokarin kare martabar kasarsu a kowane hali. Amma yayin da suka tsinci kawunansu a karkashin shugabanni a kowane mataki suna wulakantasu ba za su dauki kasar da muhimmanci […]
Dasa kishin kasa a zukatan ‘yan kasa yana sa kishin kasa, kuma hakan yana daya daga cikin dalilan da suke sa wa a tarar da mutane suna kokarin kare martabar kasarsu a kowane hali. Amma yayin da suka tsinci kawunansu a karkashin shugabanni a kowane mataki suna wulakantasu ba za su dauki kasar da muhimmanci ba.
Kishin kasa yana tafiya tare da kare mutunci da sanin mutunci kai da ’yan kasa, ba yadda wasu kasashe za su yarda a rika jibge masu kayan gwanjo, sai dai su nemi hanyoyin da za su rika kira ko sarrafa nasu.
Wannan sabanin yadda Najeriya take inda ake kawo kowane irin gwanjo da gumama ana zubewa a cikin kasar, ba a iya sayen sabo sai na hannu! Ko abincin da za a ci a cikin gida sai an shigo da shi, ko nama sai an shigo da shi daga Nijar ko Kamaru.Haka kayan da za a sa, kuma hakan ya tabbatar da cewa Caina ta mayar da Najeriya babbar kawa.
A kan haka maimakon a koya wa mutane yadda za su kama kifi, sai dai a ba su kifin, wannan halayar ta zama ita ce wadda shugabanni da ’yan kasuwa da malamai sukan yi aiki da ita. Su kansu ’yan siyasa maimakon koya wa matasa sana’o’i, sai dai a ba su kudi! Ta yadda maimako a yi noma sai dai mu saya daga wajen manona, maimakon a kafa kamfani sai dai a shigo da sarrafaffun kaya. Ya kamata mu koya daga kasashen da suka ci gaba kamar su Caina da Indiya da Jamus da sauransu.Yana da kyau mu dubi wasu hanyoyin da suka yi amfani da su suka zama kasashe masu tsayuwa da kafafuwansu.
Wani abu mai muhimmanci shi ne ’yan kasa su san darajar tutar kasa wadda babbar alama ce a kowace kasa. Inda ko a kasar nan a tashin farko kusan duk yunifom din ’yan makaranta launin tutar kasar ne, hatta fentin gine-ginen gwamnati da wasu mutane masu kishin kasar.
Idan muka lura ko uba ne, duk talaucinsa za ku iske ’ya’yansa suna girmama shi da kallon mutuncinsa, idan sun san yakan yi iya kokarinsa wajen kula da su tare da wadata su da abin dake hannunsa. Amma idan ya ki kula da su ko yana nuna bambanci tsakanin ’ya’yansa da ’ya’yan ’yan uwa ko makwabta dole a samu sabani.
Idan ana son dawo da kishin kasa a Najeriya sai an rage zuwa kasashen waje don karo karatu ko kula da kiwon lafiya.Ya kamata mu dogara da kanmu, kuma a karfafa wa kananan ’yan kasuwa da jarin da za su kafa kamfanoni don a rage dogaro da kayan kasashen ketare. Tabbas a wajen shugabanni ne za mu ga irin wadannan misalan na dawo da ’ya’yansu
makarantun gwamnati da asibitocin gwamnati tare da amfani da abubuwan da ake sarrafawa a cikin gida a gidajensu.
Sannan yana da muhimmanci a rika shirye-shirye na wayar da kai a gidajen talabijin da na rediyo don mutane su gane hanyoyin kishin kasa da amfaninsa. A rage ko guji irin shirye-shiryen nan da za ka ji ana
yaba wa wasu kasashen da ba su kai Najeriya daraja ba, don haka yana hana hobbasa. Domin duk yadda za ka kushe Najeriya za ka tarar kasa ce abin yabawa idan ka kwatanta da wasu kasashe. sannan Allah yana son kasar shi ya sa kasar ta tsallake matsaloli da dama, kai wasu ma sun yi hasashen cewa kasar bana za ta ruguje, amma cikin ikon Allah sai kara dunkulewa take yi.
Aure tsakanin kabilu shi ma wani abu ne da zai sa so da kauna tsakanin ’yan kasa, musamman kasa irin Najeriya mai kabilu da dama a warwatse a cikin kasar.
Saboda haka lokaci ya yi da za mu dawo da kishin kasa a zukatanmu ta haka ne za mu kula da al’amuran kasar yadda ya kamata. Kai ma za ka iya yin kishin kasarka, kuma haka zai daga darajar kasar da kai kanka a idon duniya. Hanyar da za mu bi ita ce ta hanyar jan hankalin ’yan kasa da kishinsu, tare da bai wa jami’an tsaro horo su sani kasar suke bautawa ba wai aljihunsu ba, bayan an kara albashi da abubuwan more rayuwa tare da nuna wa mutane muhimmancin ayyukansu. A sani a kowane aiki za a iya shiga aljana ko wuta! Kuma
tabbas sai an rika horo da hukunta mabarnata tare da kyautata wa duk wadanda suka yi wani yunkuri da kawo ci gaba ko ceton kasar da ’ya’yanta daga fadawa cikin wani hali na nakasu.
A halin yanzu babu kasar da ’yan kasar ba su kishinta kamar Najeriya, a kan haka sai mu taya zababben shugaban kasa da addu’ar Allah ya ba shi ikon aiki da fito da kasarmu daga halin da ta fada, ta yadda za mu rika kishin kasar.
Buhari Daure
Muryar Talaka
kofar kaura, Katsina
+2347035986444