Hanyoyin inganta al’umma ta fannin Kimiyya da kere-kere (2)

Fannoni Masu Muhimmanci Ga duk wanda ya dubi al’ummar Najeriya gaba dayanta, da al’ummar arewacin kasar nan musamman, ya san lallai muna da matukar bukatuwa zuwa ga wasu fannoni na musamman da suka shafi ilmi, Wadanda ko dai samuwarsu ne zai kawo mana ci gaba kai tsaye, ko kuma ta hanyar samuwarsu rayuwa za ta […]

Hanyoyin inganta al’umma ta fannin Kimiyya da kere-kere (2)

Likita na duba kwayoyin halitta

Fannoni Masu Muhimmanci

Ga duk wanda ya dubi al’ummar Najeriya gaba dayanta, da al’ummar arewacin kasar nan musamman, ya san lallai muna da matukar bukatuwa zuwa ga wasu fannoni na musamman da suka shafi ilmi, Wadanda ko dai samuwarsu ne zai kawo mana ci gaba kai tsaye, ko kuma ta hanyar samuwarsu rayuwa za ta inganta har a karshe a samu ci gaba bayyananne.  Muna da bukatuwa a fannin likitanci a kasar nan.  Muna da bukatuwa zuwa ga kwararrun likitoci a kasar nan.  Kamar yadda Dakta Solomon Anyegwu, shugaban kungiyar Masu Lura da Muhalli na kasa ya sanar da manema labaru a shekarar 2012, cikin mutum miliyan 150 da kasar nan ke da su a kalla, likitocinmu guda dubu 35 ne!  Wannan ke nuna kowane likita daya zai lura da marasa lafiya dubu 3,800 ke nan, da a ce kowa zai kamu da rashin lafiya a lokaci guda.  Wannan ko kusa bai yi ba da ka’idar Majalisar dinkin Duniya da ya ce a samu likita guda ya rika lura da mutane 600.
Bayan fannin likitanci, fannin kere-kere ma yana matukar bukatar kwararru na musamman, musamman a Arewacin Najeriya, Wadanda za su dada inganta mana sana’o’inmu da muka tashi muka ga kakanninmu a kai.  Babban abin bakin ciki shi ne yadda muka wayi gari kowa ya kaurace wa sana’o’in gargajiya da muka gada daga iyaye.  Wadanda suka gada suna yi kuma sun kasa inganta su.   Misali, baa bin mamaki bane har yanzu ka ga makera na amfani da kayayyakin aiki irin na baya.  Hakan ba aibu bane dari bisa dari, amma da za a inganta sana’ar, ta hanyar amfani da kayayyakin zamani, wannan zai dada jawo abokan huldar ciniki (kwastoma), ya kuma saukake wa mai sana’ar hanyoyin kere-kerensa.  Sana’o’i irin su kira, da saka, da rini suna da matukar amfani wajen gina al’umma; ko dai wajen samar da sana’a ko inganta rayuwa ta hanyar samar da hanyoyin more rayuwa.
Har wa yau muna da karancin malamai a dukkan wadannan fannoni a makarantunmu, musamman a fannin kere-kere. A wani bincike na musamman da wani malamin jami’a yayi a jihar kogi, yace ba abin mamaki bane ka samu dalibin da ke karanta fannin kere-kere musamman a fannin karafa, amma bai san bambancin da ke tsakanin noti (Nut) da sandar noti (bolt) ba.  Duk da cewa wannan bangare ne da ya shafi hukuma, amma mu kanmu ba mu mayar da hankali wajen karatu. Domin bincike ya nuna cewa duk yadda al’umma ko wani yanayi ko dama ta baci, idan mai nema ya mayar da hankalinsa, ya sa abin a ransa, zai dace.

Duk kwakwalenmu Iri daya ne
Cikin shekarun da nayi ina rubutu a wannan shafi na sha samun tambayoyi kan yadda turawa ke samar da na’urori masu aiwatar da abubuwa cikin mamaki da al’ajabi, da cewa: “Shin, wannan ba sihiri ne suke yi ba kuwa?”  Haka ma cikin shirin da Sunnah Tb ke shiryawa wanda suke hira da ni kan hanyoyin sadarwa, daga cikin masu tambaya akwai wanda ya yi tambaya makamanciyar haka, sadda na gama bayani kan tsarin sadarwar wayar iska, da fasahar Bluetooth, da Infra-red da dai sauransu.   Suna ganin ba abu ba ne mai yiwuwa a ce ka kira mutum a waya daga garin Kaduna, wanda kake kira kuma yana wata kasa ko wata jiha daban, cikin ‘yan dakiku wayarka ta fara ruri tana kiransa, kuma ace tsakanin sadda ka latsa wayarka ka fara kiransa, zuwa lokacin da kiran ya shiga wayarsa, sai da na’urar sadarwa ta dauki bukatarka zuwa rumbun bayanan kamfanin wayarka, kamfanin wayarka kuma ta cilla wa kamfanin wayarsa.  Daga nan kuma kamfani wayarsa ya nemo jiha ko bigiren da mai waya yake, kafin ta sadar masa.  Shin, wannan ba sihiri ba ne kuwa?
Amsar da nake bai wa masu tambaya makamancin wannan ita ce, tsari irin wannan, wanda ke samar da na’urorin kere-kere na sadarwa ko na safara, ko na gine-gine, duk ba sihiri ba ne.  Ilimi ne tsantsa!
Za mu cigaba