Hanyoyin kara tsawon gashi

Mata da yawa na son ganin gashinsu ya kara tsawo, hakan ba zai samu ba har sai sun rika kula da gashinsu, kasancewar gashi na kara wa mace kyau. Akwai hanyoyi da dama wadanda muka kawo miki a yau, idan kika bi su sau da kafa za su taimaka miki wajen kara wa gashinki tsawo, […]

Hanyoyin kara tsawon gashi
Hanyoyin kara tsawon gashi

Mata da yawa na son ganin gashinsu ya kara tsawo, hakan ba zai samu ba har sai sun rika kula da gashinsu, kasancewar gashi na kara wa mace kyau. Akwai hanyoyi da dama wadanda muka kawo miki a yau, idan kika bi su sau da kafa za su taimaka miki wajen kara wa gashinki tsawo, baki da yalki da kuma karfi. Wani abu dangane da wadannan hanyoyin shi ne, ba sa bukatar ki kashe kudi.
·         Daga farko ki dora man kwakwa a wuta sannan sai ki zuba masa man amla. Daga nan sai ki gauraya sosai, idan kin tabbata sun gaurayu, sai ki sauke daga wuta, har hadin ya huce. Sai ki zuba man a kwalba ko murta. Kina shafa wannan hadin a fatar kanki da gashinki kamar sau uku a sati.
·         Lemun tsami na sanya tsawon gashi sosai. Ki samu ruwan lemun tsami, sai ki hada shi da kwai da kuma man amla. Sai ki shafa hadin a fatar kai da kuma gashi. Ki bar hadin a kanki har tsawon minti 30, sannan ki wanke da ruwan dumi. Za ki iya yin wannan hadin sau 2 a wata.
·         Ki samu ruwan Aloe bera, sai ki shafa a fatar kai da kuma gashi, bayan minti 20 sai ki wanke da ruwan dumi.
·         Man zaitun na sanya gashi ya yi baki, taushi da kuma tsawo. Za ki iya mayar da man zaitun ya zama man kitsonki.
Muna so ku san cewa za ku iya zabar daya daga cikin wadannan hanyoyin, domin kowace hanya za ta biya miki bukata. Idan kuwa kika yi amfani da gaba dayansu, za su iya sanya a garin gyaran gira ki rasa ido. Muna fata za ku yi hutun karshen mako lafiya.