Hanyoyin kasuwanci da samun kudi don matasa
Yadda za ku iya yin kasuwancinku kuma ku samu kudi a matsayinku na matasa a Najeriya
Shin kun san za ku iya yin kasuwancinku kuma ku samu kudi a matsayinku na matasa a Najeriya?
Zan nuna muku yadda abin yake a cikin wannan rukunin mudawwanai zalla, wato Blogs a sakonnin intanet da ke kasa.
- NAJERIYA A YAU: Laifin Wane Ne Rashin Daukar Masu Digiri Aiki a Najeriya?
- Ban yi wa sassan jikin Hanifa gunduwa-gunduwa ba —Abdulmalik Tanko
- Giwa ta murkushe wani dan Saudiyya a Uganda
Don haka, a gyara wurin zama, a samu kofin shayi a natsu kuma ku shirya don fara samun kudi!
A matsayin matashi a Najeriya, za ka iya samun kudi ta wasu hanyoyin kasuwancin intanet kamar:
Aiki da za a yi a samu kudi ta amfani da kasuwancin intanet ta hanyar Fiverr da kafar kasuwancin intanet ta Upwork da sauran kafafen tallace-tallace.
Ana iya zama mamallakin masarrafa don bude taska a intanet (Blogger) da yin aiki mai zaman kansa don samun kudi, fara bude tashar bidiyo na YouTube da tashar yada labarai ta intanet.
Zayyanar hotuna (Graphic design)
Idan kai kwararre ne a harkar fasaha kuma kana son fasaha, za ka iya shiga kasuwancin zayyanar hotuna.
Kana iya farawa ta hanyar yin tsari mai sauki amma kananan zayyana da za a iya buga su a jikin rigunan T-shirt don abokanka da danginka, sannan ka sanya shi cikin kasuwanci.
Hakanan, za ka iya yin wasu ayyuka masu zaman kansu don tallar kasuwanci na gida a yankinka.
Bude taska a intanet (Blogging)
Tare da karamin ilimin fasaha da wasu kwarewar rubutu da mukalolin da aka zaba, za a iya fara kasuwanci ta hanyar bude Mudawwanai (blog). Wannan tunanin kasuwanci yana daukar dan lokaci don samun riba.
Don farawa, ana bukatar habaka masu sauraro, sannan a samu damar hadin gwiwa tare da masu talla da abokan hadin gwiwa don samun kudaden shiga.
Idan za su iya inganta blog dinsu, kodayake, wannan na iya zama hanya mai sauki don samun karin kudi a gare ka a matsayin matashi.
Kafar Yada Labarai ta intanet (Podcasting)
Kafar yada labarai ta intanet sabuwar fasaha ce ta take habaka!
Yana kama da bude taska da rubutun ra’ayin kanka a intanet. Duk abin da ake bukata shi ne sha’awar takamaiman mukala da kuma habaka adadin mabiya shafin, amma wanda aka yi.
Za ka iya fara samun kudin shiga ta hanyar nemo masu talla wadanda ke da sha’awar wallafa tallace-tallace a shafin da yada muryar tallanku ta intanet.
Mayar da bayanan sauti ko bidiyo zuwa rubutu (Transcription)
Ana iya mayar da bayanan sauti ko na bidiyo zuwa rubutattun bayanai wata hanyar kasuwanci ce da za a iya bayyanawa.
Akwai bukatar aiki akan kwarewar rubutu, daidaito da saurin yin rubutun.
Hotuna (Photography)
Mutane suna shirya bikin aure, taron karawa juna sani da taron musamman da taron nuna bajinta da tunawa da juna da taron karshen mako.
Kowace rana ranar haihuwar wani ce kuma har an samu kyamara me canza launuka wanda zai so a tuna da ranarsu ta musamman da aka dauka kuma a nan ne inda ake shigo da hoto.
Abin mamaki ne? Kana zuwa makaranta daga Litinin zuwa Juma’a kuma ba ka da aiki a gida a karshen mako?
Me zai hana ka ajiye wasu kudi ka tuntubi iyayenka kuma ka samu wayar hannu ko kyamara?
Mutane suna amfani da wayoyin hannu don daukar hotuna masu ban mamaki a kwanakin nan. Kasancewar dalibi shi ne ya sa ya kamata ka samu fasahar samun kudi da ita domin ban taba ganin rukunin mutane masu son daukar hoto fiye da dalibai ba.
Me ya sa ba za su arzuta kansu da sha’awar hotuna ba?
Rubutun kashin kai
Lokacin da kake mai zaman kanka, ba dole ba ne ka yi aiki don mutum daya kawai.
Za ka iya samun abokan ciniki da yawa kamar yadda lokacinka zai iya ba ka.
Idan kana da kwarewar rubutu, wannan bangaren naku ne kuma ku yi tsammani menene?
Ba zai cutar da lokacin masu neman ilimin ku ba. Za ka iya yin aiki a lokacinka da kake bukata.
Na ji kuna rada, “Amma ban san yadda ake rubutu ba?” Ya ce, waye?
Wane ne yake yi muku ayyukan da kuke yi a makaranta lokacin da aka ba ku wani maudu’i, idan aka ce ku yi bincike a kansa kuma ku rubuta da kalmominku?
Na tabbata kana rubuta jarrabawar da Ingilishi kuma kana rubuta wasiku da kanka, don haka babu abin da zai hana ka rubutun kudi a matsayin marubuci mai zaman kansa.
Duk abin da kake bukatar yi shi ne yin bincike a kan wani batu kuma ka sake rubuta wa cikin kalmominka bayan tattara bayanai daga shafuka masu yawa.
Yin rubutu kai-tsaye? Abokan hulda za su gaya maka abin da suke so ta fuskar salon rubutu, adadin kalmomi, sauti da sauran bayanai.
Yin kyandir
Yin kyandir sana’a ce mai sauki wadda akoyaushe ake bukata.
Don haka, a matsayin matashi mai neman tunanin yin kasuwanci wanda za a iya sayarwa, don saukin koyo da karamin jari na farawa, to wannan yana iya zama a gare ka. Ana iya koyon yin kyandir ta hanyar kallon bidiyo a tashar YouTube ko koyo daga wani gwani.
Fara bude tashar YouTube
Fara bude tashar YouTube na iya ba ka kudi da yawa a matsayinka na matashi a Najeriya.
Ya zuwa yanzu, muna da matasa da yawa wadanda ke samun daloli a YouTube.
Kana iya samun kudi lokacin da mutane ke kallon bidiyonka a kan tasharka ta YouTube.
Babban mabudin zama mamallakin tashar (youtuber) shi ne samun abin sha’awarka, kana bukatar sanin abin da mutane ke burge su kuma ka samu kudi daga gare su.
Yana iya zama wasan ban dariya da koyar da rawa da koyar da girke-girke da sauransu.
Hakanan, idan burinku a matsayin mamallakin tashar youtube shi ne a samu masu biyan kudi 1,000 da samun masu kallo 4,000 a cikin sa’o’i, a cikin shekararka ta farko idan kana shirin samun kudi daga wannan hanyar za ka iya samu.
Noma
Noma wata sana’a ce a Najeriya ga matasa da manya mutane. Matasa kadan ne suka san za su iya samun kudi ta hanyar noma.
A nan akwai wasu hanyoyin noma don samun riba kamar: kiwon kifi, kiwon dodon kodi, noman ganyayyaki da dai sauransu.
Yankinka na iya tantance nau’in noman da za ka iya shiga. Mutanen karkara za su iya shiga kusan kowane nau’in noma.
Kiwon kajin da za a sayar a lokacin bukukuwa hanya ce mai kyau da za ka iya samun kudi a matsayinka na matashi.
Abin da kawai za ka yi shi ne gano nau’in noman da zai yiwu a cikin al’ummarka ko yankin ka ko gidan ka.
Yi bincikenka kuma ka samu dan jari kadan daga iyayenka don farawa.
Don haka, ina so in yi tambaya, shin kun yanke shawarar kowace fasaha ko tunanin kasuwanci da kake son yi a matsayin matashi?