Hanyoyin Kauce wa Husumar Auratayya (2)

Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili.   Da fatan Allah Ya amfanar da mu duk bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan hanyoyin kauce wa faruwar husuma tsakanin ma’aurata. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.1. […]

Hanyoyin Kauce wa Husumar Auratayya (2)
Hanyoyin Kauce wa Husumar Auratayya (2)

Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili.   Da fatan Allah Ya amfanar da mu duk bayanan da za su zo cikinsa, amin.
 Ga bayani kan hanyoyin kauce wa faruwar husuma tsakanin ma’aurata. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
1. Abu na hudu da zai taimaka ga ma’aurata wajen kauce wa faruwar husuma cikin rayuwar aurensu shi ne yawan kawar da kai ga kananan abubuwa; kamar yadda halin ma’aurata ya sha bamban, to dole ne kuma dabi’a ta bambanta; ta iya yiwuwa akwai wata dabi’ar maigida da take tsananin bakanta ran uwargida; shi kuma wannan dabi’a ta riga ta kama shi sosai da har ba zai iya dainawa ba; maimakon uwargida ta yi ta wahalar da kanta tana jin haushi, ranta na baci duk lokacin da maigida ya yi abin nan da bata so, sai ta sawwaka wa kanta, ta kawar da kai da zuciyarta daga abin, ta daina bari yana bata mata rai in ya faru; in ma har ranta ya baci ta yi kokari nan da nan ta kawar da bacin ran daga zuciyarta ta hanyar tunawa cewa ba wani alfanu da bacin ran nan zai haifar mata sai dai rashin alfanu ta hanyar rage mata kwanciyar hankali da dadin zamantakewa da mijinta.
2. Abu na biyar shi ne ma’aurata su dage ga yin hakuri da abubuwa marasa dadi duk na cikin aure da na rayuwa gaba daya; hakuri maganin zaman duniya ne, musumman kuma maganin zaman aure; in dai ana son aure ya rayu dole sai an hadiyi magani mai tsananin daci na hakuri.
3. Yin kyakkyawan zato wa juna shi ma hanya ce ta kauce wa faruwar husuma tsakanin ma’aurata; domin zai hana su fadawa cikin fargaba da tashin hankalin da mummunan zato ke haifarwa, wadanda duk sinadarai ne masu rura wutar husumar auratayya.
4. Kauce  wa zargin juna ba tare da wata cikakkiya ko kwakwarar hujja ba shi ma yana taimaka wa ma’aurata kauce wa faruwar husuma a tsakaninsu.
5. Rufa wa juna asiri; shi ne kada ma’aurata su rika yamadidin yada sirrikan abokan aurensu ga wasu daban koda kuwa iyaye ne ko ’yan uwa makusanta. Kada uwargida ta rika labarta kura-kurai da raunin mijinta ga ’yan uwa ko kawayenta. Haka shi ma maigida kada ya je yana fadar laifuffukan matarsa ga ’yan uwa ko abokansa. Allah kadai Ya kamata ma’aurata su rika kai karar kura-kuran abokan aurensu gare Shi domin Shi ne Zai daidaita musu al’amuransu kuma Shi ne Zai shiryar da su Ya ganar da su su daina aikata wadannan kura-kuren.
6. Sannan ma’aurata za su iya kauce wa husuma cikin rayuwar aurensu ta hanyar dabi’antuwa da kankan da kai da saukaka wa juna tsakaninsu; wani lokacin ’yar karamar kalma daya da aka furta da kyakkyawan lafazi, ko dan karamin murmushi da aka yi da kyakkyawar niyya na iya kwantar da wutar husumar da ta fara kunnuwa yanke. Amma hali irin na jiji da kai, nuna isa da fin karfi da kuma kowa na kokarin ya fi dayan abubuwa ne su ke rura wutar husuma wacce za a yi ta faman kashewa ta ki mutuwa har sai daya ko duk ma’auratan sun saduda sun janye sannan husumar ta lafa. Don haka sai ma’aurata su dage su kori duk irin wadannan halaye daga cikin auratayyarsu musamman in suka yi la’akari da cewa ba su haifar musu wata riba sai asara a cikin zamantakewar aurensu.
7. Wata hanyar kauce wa faruwar husuma  a rayuwar aure ita ce koyaushe ma’aurata su rika zabar zaman lafiyar rayuwar aurensu sama da so ko ra’ayin zukatansu da bukatunsu; duk wani abu da maigida yake so shi kadai wanda zai kawo cikas ga dorewar zaman lafiyar aure, to ya kamata ya hakura da shi haka ita ma uwargida.
8. Haka nan ma’aurata za su iya kauce wa faruwar husuma cikin rayuwar aurensu ta hanyar yin ’yar karamar rigima a kai-a kai in ta kama, domin ’yar karamar rigima ba mai zafi ba tana kara dankon zamantakewa kuma tana hana ruruwar gagarumar husuma.
9. Sannan ma’aurata za su iya kauce wa faruwar husuma cikin rayuwar aurensu ta hanyar narkar da sanyin daskararriyar husuma a tsakaninsu; daskararriyar husuma ita ce ma’aurata za su kasance kamar suna zaune lafiya a fili, amma a can ciki kowa na cike da haushin kowa, amma ba mai nuna wa wani da baki sai dai ta hanyar share juna da rashin kulawa da rashin darajta juna. Illar da daskararriyar husuma take haifarwa ta fi na husuma ta zahiri; sannan duk ranar da ta narke, to da wuya a samu wani abu mai kyau a cikin wannan dangantaka. Don haka ma’aurata su guji barin husuma ta  daskare na kwana uku a tsakaninsu.
Sai  mako na gaba in sha Allah.   Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.