Hanyoyin kula da jiki

Gangar jikinmu abu ne da yakamata mu rika kula da shi domin kare lafiya da kuma jin dadinmu.. In ba haka ba za a iya haduwa da cututtuka da dama. Mata musamman wadanda suka haihu yakamata su san yadda za su rika kula da jikinsu haka kuma idan suna da sabon ciki akwai abubuwan da […]

Hanyoyin kula da jiki

Gangar jikinmu abu ne da yakamata mu rika kula da shi domin kare lafiya da kuma jin dadinmu.. In ba haka ba za a iya haduwa da cututtuka da dama. Mata musamman wadanda suka haihu yakamata su san yadda za su rika kula da jikinsu haka kuma idan suna da sabon ciki akwai abubuwan da za su yi domin rage harar da duk abin da suka ci. Wasu na da yawan gumi, wasu kuma warin jiki ne da su da dai sauransu. A yau na kawo muku hanyoyin da za a bi ne domin magance wadannan matsalolin.

· Yawan gumi; a samu ruwan amfuna da zuma a zuba a ruwa a kasance ana sha a kullum domin rage yawan gumi. Ko kuma a hada garin ‘baking soda’ da man zaitun da ruwa a kwaba sannan a rika shafawa a inda gumin ke yawan fita. Yawan shan bakin shayi da lemun tsami da man kwakwa na rage fitowar gumi a jiki.

Warin jiki; idan ka kasance mai warin jiki za a iya hada garin ‘baking soda’ da ruwan lemun tsami a kwaba sannan a shafa a hammata da wuraren da ke yawan wari a jiki na tsawon mintuna biyar sannan a yi wanka.

·Mace mai juna biyu;  gari na wayewa ta sha ruwa kofi daya kafin komai. Ta samu citta ta markadata sannan ta zuba ruwa ta dora a wuta ya tafasa na tsawon mintuna goma sannan tat ace a zuba zuma ta sha a kalla kofi biyu kullum da safe.

· Kodewar fata saboda rana; za a iya samo ganyen ‘aloe bera’ a  matse ruwan a inda kunar ta shafa na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke. Ko kuma a samu madarar gari da zuma a kwaba a shafa a wajen kunar na tsawon awanni biyu kafin a shiga wanka.

· Zanen ciki (Stretch marks); wannan irin zane na bayyana ne a jikin mace sakamakon cikin da ta dauka. Bayan ta haihu wasu ba su san yadda za su magance wadannan matsaloli ba. A samu ruwan kwai sannan a shafa a zanen daya bayanan, a rika shafawa a ciki  da cinya da sauransu. A jira ruwan kwan ya bushe kafin a wanke. Za a rika yin haka ne a kullum.

·Yawan bushewar lebe; a samu man ‘glycerin’ da lemun tsami sannan a kwaba sannan  a shafa a lebe kullum da dare kafin a kwanta barci. Yin hakan zai sa a samu lebe ya yi santsi da kuma laushi.