Hanyoyin kula da jiki

Gangar jikinmu abu ne da ya  kamata mu kula da shi domin samun jin dadi. In ko ba haka ba za a hadu da cututtuka da dama. Mata musamman wadanda suka haihu ya kamata su san yadda za su kula da jikinsu haka kuma idan suna da sabon ciki akwai ababen da za su yi […]

Hanyoyin kula da jiki

Gangar jikinmu abu ne da ya  kamata mu kula da shi domin samun jin dadi. In ko ba haka ba za a hadu da cututtuka da dama. Mata musamman wadanda suka haihu ya kamata su san yadda za su kula da jikinsu haka kuma idan suna da sabon ciki akwai ababen da za su yi domin rage hararwa da duk abin da suka ci. Wadansu na yawan gumi, wadansu kuma warin jiki ne da su da sauransu. A yau na kawo muku hanyoyin da za a bi domin magance wadannan abubuwa.

  • Yawan gumi: A samu ruwan amfuna da zuma a zuba a ruwa a kasance ana sha a kullum domin rage yawan gumi. Ko kuma a hada garin ‘baking soda’ da man zaitun da ruwa a kwaba sannan a rika shafawa a inda gumin ke yawan fita. Yawan shan bakin shayi da lemun tsami da man kwakwa na rage fitowar gumi a jiki.
  • Warin jiki: Idan kin kasance mai warin jiki za a iya hada garin ‘baking soda’ da ruwan lemun tsami a kwaba sannan a shafa a hammata da wuraren da suke yawan wari a jiki na tsawon minti biyar sannan a yi wanka.
  • Mace mai juna biyu: Gari gari na wayewa ta sha ruwa kofi daya kafin komai. Ta samu citta ta markada ta sannan ta zuba ruwa ta dora a wuta ya tafasa na tsawon minti goma sannan a tace a zuba zuma ta sha akalla kofi biyu kullum da safe.
  • Kunar rana/ kodewar fata: Za a iya samo ganyen ‘aloe bera’ a matse ruwan a inda kunar ta shafa na tsawon minti ashirin sannan a wanke. Ko kuma a samu garin madara da zuma a kwaba a shafa a wajen kunar na tsawon awa biyu kafin a shiga wanka.
  • Nankarwa (stretch marks): Wannan layin na bayyana ne a jikin mace sakamakon cikin da ta dauka. Bayan ta haihu wadansu ba su san yadda za su magance wadannan matsaloli ba. A samu ruwan kwai a shafa a wajen da nankarwar ta bayyana kamar su tumbi da cinya da sauransu. A jira ruwan kwan ya bushe kafin a wanke. Za a rika yin haka a kullum.
  • Yawan bushewar lebe: A samu man ‘glycerin’ da ruwan lemun tsami a kwaba su a shafa a lebba kullum da dare kafin a kwanta barci. Za a samu lebe mai sulbi da kuma laushi.