Hanyoyin kula da lafiyar gajiyayyu
A makon da ya wuce mun ga hanyoyin kula da tsofaffi ta hanyar kiyaye yawan faduwa da buguwa. A yau za mu duba yadda za a kula da lafiyar gajiyayyu. A nan ana nufin gajiyayyu wadanda suke da nakasu a kwakwalwa.Irin wadannan gajiyayyu kan shiga halin rashin lafiya ba tare da masu kula da su […]
A makon da ya wuce mun ga hanyoyin kula da tsofaffi ta hanyar kiyaye yawan faduwa da buguwa. A yau za mu duba yadda za a kula da lafiyar gajiyayyu. A nan ana nufin gajiyayyu wadanda suke da nakasu a kwakwalwa.
Irin wadannan gajiyayyu kan shiga halin rashin lafiya ba tare da masu kula da su sun lura ba, tunda a mafi yawan lokuta ba su iya bayani, domin maganarsu idan ma ta fito akan ji kamar gwaranci. A da an fi ganinsu a gidan gajiyayyu na hukuma, inda ma’aikata na musamman ke kula da su. Amma yanzu sun fi yawa a gida, wadanda iyayensu ne suke kula da su, watakila ko don gajiyawar gwamnati. A yanzu a irin wadancan gidajen an fi ganin marayu. A wani bincike da aka gudanar a Asibitin koyarwa na Zariya a bara, an nuna cewa fiye da rabin yara da manya da ke zuwa bangaren kwakwalwa na asibitin ne ke fama da wannan matsala.
Ga matsalolin da wadannan bayin Allah suka faye samu da kuma hanyoyin da za a kiyaye su ko magance su:
1-Yawan Dalalar Miyau: Yawan dalalar da yawu tana daya daga cikin babbar matsalar irin wadannan gajiyayyu, wadda idan ba a dauki mataki ba za ta iya jawo kwayoyin cuta shiga baki da hanyoyin numfashi su rika yawan mura da ciwon hakarkari na lumoniya. Yawan goge musu baki da burushi da makilin da tsane musu miyau ta hanyar saka mayanin nan na wuya, wato bib zai taimaka. Idan matsalar tana jawo yawan mura da tari dole sai an je asibiti an karbi maganin rage dalalar da yawu. Wato ke nan kai irin wadannan marasa lafiya bangaren kwakwalwa na manyan asibitoci a kai-a kai zai taimaka musu kwarai da gaske.
2-Yawan fitsari: Yawan fitsarin kwance ko ma na zaune zai iya jawo kwayoyin cuta shiga mafitsara. Don haka tsabtar abin shimfida da abin zama tana daya daga cikin babbar hanyar kiyaye hakan. Akan iya amfani da leda wadda aka rufe da zani a wurin zama da kwanciya, sa’annan a rika lura da fatar cinyoyi ana shafa hoda don kada fitsari ya cinye wurin. A nemi abin auna dimin jiki a kyamis a saya a ajiye a gida domin auna dimin jikinsu bayan kwana biyu-biyu ko uku-uku. Duk lokacin da aka ga makin ya haura 37 ko da da digo daya ne, a kai su asibiti a duba su.
3-Yawan kwarewa/Shakewa: A lokuta da dama idan aka ba irin wadannan abinci ana so a zaunar da su na tsawon sa’a kafin kwanciya domin abinci ya samu ya shige uwar hanji. Idan ba a haka, wato idan ana ci aka kwantar, za a iya samun yawan kwarewa yadda abinci ko abin sha zai gangaro ya bi hanyar iska.
4-Yawan Taurin Bayan Gida: daya daga cikin abin da ke sa bayan gida laushi shi ne yawan kazar-kazar. A masu irin wannan matsala wadanda suke zaune ko kwance wuri daya ana yawan samun matsalar taurin bayan gida, don haka sai ana yawan ba su ruwa sosai, ko wani abin sha, da hada musu da kayan ganye da na marmari a abinci. Idan aka kwana fiye da uku ba su yi bayan gida ba, alama ce ta cewa bayan gida ya yi tauri ya makale sai an je asibiti an cire. Wasu ma akan koya musu yadda ake cirewar idan suna son koyo.
5-Yawan Jijjiga: Masu wannan matsala sun fi kowa shiga hadarin samun yawan jijjiga wadda za ta iya kai wa ga suma da mimmikewa. Akan so idan irin wannan ta faru mai kula da su ya yi maganin abin ba sai an je asibiti ba, tun da abu ne da zai rika faruwa yau da gobe. Don haka yana da kyau mai kula da irin wadannan ya koyi yadda ake wa masu jijjiga, wato a kwantar da su a kasa, a gefen dama ko hagu, a tabbata ba su tauna harshe ba, ta hanyar haskawa da duba baki. Idan suna cikin cin abinci ne sai an yi maza an cire abin da ya rage a bakin kada ya shake su. A kuma san yadda ake ba da maganin jijjiga ta hanyar dauke, wato wanda ake cusawa ta dubura, ba na sha ba. Ya kasance a kodayaushe akwai wannan magani a gida idan marar lafiyar mai yawan jijjiga ne.
6-Rashin Samun Isasshen Abinci: Akwai masu wannan matsala wadanda tauna da hadiya ma wahala take musu. Irin wadannan ba a cika so a ba su abinci mai tauri ba sai dai mai ruwa-ruwa kamar na yara amma mai karin kuzari irin su abincin nikakkiyar gyada da waken soya da gero a ciki ko masara, wanda aka fi sani da tom brown, wato kunu ko kamu mai dauke da abubuwa da dama. A wasu lokuta in ba sa karba sai an kai ga asibiti an sa robar cin abinci, wadda ita ma idan aka sa ta sai an koyar da yadda za a ba da abincin ta robar. Akan kuma iya ba da ruwan magungunan bitaman.
7-Rashin Wasanni: Irin wadannan nakasassu suna da son wasa sosai domin ko yaya aka musu wasa sukan ji dadi da fara’a, wasu ma su rika kyalkyala dariya. Wannan na cikin abin da kan faranta musu rai, don haka komai za a musu a rika musu da raha da wasa kada a daure fuska. A rika koya wa yaran gida yadda ake musu wasa domin su taya mai kula da su.
8-Rashin Ilmi: Duk da ana ganin kamar irin wadannan nakasassu ba za su iya koyon komai ba, saka su a makarantu na gajiyayyu da wuri yakan taimaka wa kwakwalwarsu fahimtar rayuwa da abin da ka-je-ya-zo na yau da kullum. Don haka kada a dauka su ba za su iya koyon komai ba a ki sa su a makaranta. Bincike ya nuna akwai makarantu a yanzu masu kyau amma na kudi domin irin wadannan marasa lafiya. Muna kira ga gwamanati ma ta zage damtse ta samar da irin wadannan makarantu da ake kira special schools masu kyau a kalla ko daya-daya ne a manyan garuruwa.
Duk wasu sauran matsaloli da za su shige duhu kada a ji nauyin tambayar ma’aikatan lafiya yadda za a shawo kansu idan an je asibiti.