Hanyoyin rabuwa da kurajen ‘pimples’
Mata da yawa na fama da kurajen ‘pimples’ sun kuma rasa yadda za su rabu da su, hakan yakan sanya su cikin tsomomuwa, su kuma rasa inda za su sa kansu, saboda haka ne muka yi miki guzurin wadansu hanyoyi da za su taimaka wajen rabuwa da kurajen.– Da farko ana so awa biyu ko […]
Mata da yawa na fama da kurajen ‘pimples’ sun kuma rasa yadda za su rabu da su, hakan yakan sanya su cikin tsomomuwa, su kuma rasa inda za su sa kansu, saboda haka ne muka yi miki guzurin wadansu hanyoyi da za su taimaka wajen rabuwa da kurajen.
– Da farko ana so awa biyu ko uku kafin ki kwanta barci sai ki shafa man goge baki a fuskarki, musamman wuraren da kurajen pimples suke da yawa. Ba kowane irin man goge baki za ki shafa ba, ana so ki shafa farin man goge baki ne. Idan kin ga dama za ki iya wanke fuskarki idan man goge bakin da kika shafa ya kai minti 30, idan kin ga dama kuma za ki iya kwantawa da shi har zuwa washegari. Za ki rika maimata hakan har zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi hakan za ki ga canji a fuskarki.
– Ki kasance mai yawan shan ruwa. Haka yana da kyau duk inda za ki je ki sanya ruwa a jikin jakarki ba wai dole sai kayan kwalliya ba. Yawanta shan ruwa ba wai zai sanya miki laushin fata ba ne kawai, a’a, zai taimaka miki wajen yaki da kurajen pimples din da suke fuskarki. Haka yana da kyau ki kaurace yawanta cin abincin gwangwani, kasancewar suna dauke da wasu sinadarai da za su rika sanya kurajen fuska. Ya kamata ki rika yawanta cin ‘ya’yan itatuwa da suka hada da su abarba da lemu da ayaba da kankana da sauransu.
– Ki rika amfani da abin shafawar da ake kira ‘Antiodident spray’, irin su Jane Iradale da Neutrogenia Rapid Clear da Acne Eliminating Spot Gel da sauransu, hakan zai taimaka miki wajen daidaita man da ke fatarki, wanda masana suka ce idan ya yi yawa yakan haifar da kurajen fuska.
– Ki kasance mai amfani da man ‘Cornmeal’ a fuskarki, yakan sanya kurajen fuska su motse sannan a hankali su bace, misali man shi ne, Intagilo Clear Sal Cleanser. Sannan ki rika amfani da man da ke hana yaduwar kwayar cutar bakteriya, irin wannan man yakan ratsa kofofin da suke fatar fuskarki da ma jikinki gaba daya, sannan ya yaki kwayoyin cutar da suke fatarki, a lokaci guda ya daidaita miki yawan man da yake fitowa daga fatarki. Zai kuma cire miki kwayoyin halittar da suka mutu a cikin fatarki. Misalinsu; Phytomer Gommage da Luffa-0.