Hanyoyin rage gumin fuska
An camfa cewa kowane mai yawan gumin fuska musamman ma na hanci,masifaffiya ce ko masifaffe. Gumin fuska a likitance ana kiransa da ‘hyperhidrosis’ shi ne yake sanya yawan gumin fuska; kamar kan hanci, goshi, saman labba, wuya da sauransu. Wani za a gan shi yana da yawan gumi ba tare da ya yi wani aiki […]
An camfa cewa kowane mai yawan gumin fuska musamman ma na hanci,masifaffiya ce ko masifaffe. Gumin fuska a likitance ana kiransa da ‘hyperhidrosis’ shi ne yake sanya yawan gumin fuska; kamar kan hanci, goshi, saman labba, wuya da sauransu. Wani za a gan shi yana da yawan gumi ba tare da ya yi wani aiki ba. Akwai abubuwa da dama da suke sanya gumin fuska kamar ciwon suga, yawan kiba, hawan jini , bacin rai da sauransu.
Mata wadanda suke yawan son kwalliya za su tsane gumin fuska domin kuwa yana bata musu kwalliyarsu. Babu maganin gumin fuska amma akwai yadda za a yi domin a rage shi.
- A rage cin abinci wanda ya kunshi barkono ko kayan yaji
- Yawan shan bakin shayi na janyo gumin fuska amma za a iya shan ruwa mai yawa don ya taimaka wajen wanke duk maikon jikin.
- A rage yin amfani da man shafawa mai maiko domin irin nau’o’in wannan mai, za su dada gumin fuska. A nemi mai marar maiko domin fuska.
- Cin ’ya’yan itatuwa da ganye kamar; latas, alayyahu da sauransu, za su rage gumin fuska.
- A samu ruwan ‘binegar’ a hada da zuma mai kyau wadda ba a hada ta da sukari ba, sai a sha sau uku a rana kafin aci abinci.
- Za a iya samun ganyen ‘mistletoe’ a tafasa shi da ruwa na tsawon minti 15 sai a sha yana rage gumin fuska.
- Ganyen alkama yana da kyau wurin rage gumin fuska. A tafasa shi a sha ruwansa domin shi ganyen alkama, yana kunshe da sinadarin bitamin C da kuma bitamin B-12 wajen rage maiko da kuma gumin fuska.