Hanyoyin samun fuska mai sulbi
Akwai abubuwa da dama wanda za a yi domin samun fatar fuska mai sulbi da kuma sheki. Magance matsalolin fata na da daukar lokaci kafin a fara ganin sakamako. Don haka, yakamata idan an fara gwada irin abubuwan da muke kawo muku, sai a dan yi hakuri tukun. Wani saukin na zuwa da wuri wani […]
Akwai abubuwa da dama wanda za a yi domin samun fatar fuska mai sulbi da kuma sheki. Magance matsalolin fata na da daukar lokaci kafin a fara ganin sakamako. Don haka, yakamata idan an fara gwada irin abubuwan da muke kawo muku, sai a dan yi hakuri tukun. Wani saukin na zuwa da wuri wani kuma sai ya kai kamar watanni uku zuwa hudu kafin a fara ganin sakamako. Akwai fata da dama kamar; fata mai gautsi da mai maiko da kuma mai laushi. Saboda haka, fatan sun banbanta.
· Yawan wanke fuska na kare ta daga daukar kwayoyin cuta da dama; yana da kyau a wanke fuska kamar sau biyu a rana. Ana wanke fuskar da ruwan dumi ba mai zafi ba. Sannan a rika amfani da ruwan goge fuska (facial cleanser) ga wadanda suke da fata mai maiko. Idan har ana da gautsin fuska kuma, yana da kyau a rage yawan wanke fuskar sosai kuma kada a yi amfani da sabulai masu dauke da sinadarai masu karfi domin yin hakan zai bata fuskars.
· Yana da kyau ana amfani da dilke wajen gyaran fuska domin samun fata mai sulbi. Yin amfani da shi dilke. An fi son yin dilke kamar sau biyu a sati kuma da safe kafin a yi wanka a fita. A tabbata an jika fuskar da ruwan dumi kafin a shafa dilke a fuskar. Bayan an gama kuma, sai a wanke da ruwan dumi kafin a yi wanka.
· Ana amfani da man ‘moisturizer’ bayan an fito wanka kuma yana da kyau a rika amfani da shi kamar sau biyu a rana kuma yana da kyau a shafa a fuska lokacin da fuskar ke jike. Kuma a san irin man da ya dace a shafa a fata domin mai gautsin fata ba zai shafa man da mai maikon fata zai shafa ba da sauransu.
·Kada a manta idan an zo shafa man a fuska sai a shafa har da wuya domin kada fuska ta yi sulbi ta bar wuya da kuraje.
· Domin samun fata mai sulbi, a yi amfani da mayuka masu dauke da sinadarin ‘sunscreen’, sannan kuma a yawaita shan ruwa da kuma cin abinci masu gina jiki.