Hanyoyin Tafiyar Da Gamin Gambizar Sha’awa (1)
Hanya ta 1: Muhimman Abubuwa 5 Da Kuka Mance! Akwai wasu muhimman abubuwa da yawancin ma’aurata kan mance da shi a cikin rayuwar aurensu: ·Abu na farko shi ne mancewa da wani sirri mai maganin kowace irin matsala komai girmanta ko karfin tasirinta cikin rayuwar aure, inda ana kiyayewa da wannan muhimmin sirri ma, tun […]
Hanya ta 1: Muhimman Abubuwa 5 Da Kuka Mance!
Akwai wasu muhimman abubuwa da yawancin ma’aurata kan mance da shi a cikin rayuwar aurensu:
·Abu na farko shi ne mancewa da wani sirri mai maganin kowace irin matsala komai girmanta ko karfin tasirinta cikin rayuwar aure, inda ana kiyayewa da wannan muhimmin sirri ma, tun farko da wuya matsala mai girma ta baibaye rayuwar auren ku: wannan sirri kuwa shi ne na sanya Allah SWT sama da komai cikin rayuwar aure, da dagewa wajen yin abubuwan burge Allah SWT da neman kusancinSa sama da sauran harkokinmu na rayuwar yau da kullum. Ma’aurata su kasance cikin soyayyarsu da kaunarsu da zamantakewarsu, su sanya Allah da abubuwan neman kusancinsa, da haka da wuya su shiga cikin matsala ko halin kaka- ni- ka-yi cikin rayuwar aurensu. Misali su rika yin gasar haddar wata Surah cikin Alkur’ani mai girma, ko su rika yin azumin tadawwa’i tare, ko yin tsayuwar dare tare, da taimakon juna wajen aikata ayyukan alheri da guje wa sabon Allah.
Sannan da zarar matsala ta kunno kai, maimakon a yi ta bin Malamai da shan magungunan da ba a san kansu ba, a koma ga Allah shi ya fi. A dage da yin addu’a cikin kankan da kai da imani, cikin yardar Allah za a ga waraka daga wannan matsala. Maimakon a yi ta rokon Allah arziki da daukaka, sai a roke Shi dorewar farin ciki da soyayya cikin rayuwar aure.
Misali, ga ma’auratan da suke fama da wannan matsala ta gamin gambiza, duk cikin sujadar sallarsu su rika rokon Allah: “Ya Allah Kai ne Ubangijinmu, kuma mu bayinKa ne, Kai ne gatanmu, ba mu da wata gata bayan Ka, Ya Allah Ka gyara mana abin da ya yi tasku cikin rayuwar aurenmu, Ya Allah Ka ruruta wutar sha’awa tsakaninmu ta yadda za mu samu natsuwa da kwanciyar hankali da juna…” da sauran duk abin da suka ga yakamata su fadi na daga bukatunsu. Sannan ga macen da take fuskantar matsalar rashin motsuwar sha’awa, duk cikin sujadar kowace Sallar da ta yi, sai ta roki Allah cikin kan-kan da kai: “Ya Allah, Ubangijina, Kai ne Rayayye Mai Rayawa Mai Kashewa, Kai ne Mamallakin sama da kasa kuma Ubangijin Al’arshi Mai Girma, Ya Allah Ka wadatani da wannan Rahama da ake ji lokacin Ibadar aure, Ya Allah Ka gyara mani ko mene ne a jikina ko a halayyata da ke hana ni jin abin da ya kamata in ji a lokacin da na kadaita da maigidana…” Sai ta cike da duk abin da ta ga ya kamata na daga bukatunta ta wannan fannin. Sannan ko yaushe za a yi addu’ar nan da ma kowace irin addu’a to a bude da Salatin Annabi SAW a kuma rufe da shi sannan a rokan ma dukkan Musulmin duniya masu irin wannan matsala waraka daga matsalarsu, InshaAllah za a ga canji cikin kankanin lokaci, amma sai an dage kuma an cije, ba wai a fara a daina ba, ko kuma a yi yau, gobe a yi fashi, da fatan Allah Ya amsa mana duk bukatun mu na alheri, amin.
·Abu na biyu shi ne mancewar da kuka yi na cewa Allah SWT Bai halatta aure don a sha wuya ko a zauna cikin kunci, bakin ciki da tashin hankali ba, Allah Ya halatta mana aure don mu ji dadi kuma mu more a cikinsa, saboda haka ba wani dalilin da zai sa ma’aurata su yi ta zama cikin kunci da kaka- ni- ka- yi a dalilin wata matsala da take damun rayuwar aurensu, ya zama wajibi garesu su mike tsaye haikan don ganin sun kawar da wannan matsalar komai girmanta ko kankantarta, ya kamata ma’aurata su sa dorewar farin ciki a cikin rayuwar aurensu sama da komai a wajen mahimmanci.
·Abu na 3: Ma’aurata su tuna cewa, da zarar igiyar auren nan ta kullu tsakaninsu, to shike nan sun zama daya a ruhi da jiki, ta kowace fuska da kuma kowane bangare na rayuwarsu, dole farin cikin daya ya shafi daya. An san cewa 1 a tara da 1 amsar 2 ce, to amma ban da cikin rayuwar aure, a rayuwar aure dole koda yaushe ya kasance 1+1=1, don haka ko me daya daga cikin ma’aurata zai yi, to dole ya yi tunanin tasirin abin nan ga dan uwansa da rayuwar aurensu gaba daya.
Bai kamata ba ga daya daga cikin ma’aurata ya so kansa shi kadai, dole sai dai ya so kan sa tare da dan’uwan aurensa, bai kamata ba daya na cikin dadi da kwanciyar hankali amma dayan na cikin kunci, wani lokacin sai ka tarar ma’aurata suna nuna halin ko in kula ga halin da ’yan’uwan aurensu ke ciki, ko kuma su ma dage wajen ganin sun kuntata wa juna, don me? Wajibi ne ga ma’aurata da suke son nasara duniya da lahira cikin rayuwar aurensu su cire son rai, su guji cutar da juna, su kasance masu kula da halin da dayan suke ciki, su kuma kasance masu gaggawar yin abubuwan dadadawa juna rai, da fatan Allah Ya ba mu ikon dagewa a kan duk wani abu na kwarai, amin.
Sai sati na gaba insha Allah da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.