Hanyoyin Tafiyar Da Gamin Gambizar Sha’awa (4)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan hanyoyin tafiyar da gamin gambizar sha’awa daga inda muka tsaya a makon jiya, da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa […]

Hanyoyin Tafiyar Da Gamin Gambizar Sha’awa (4)
Hanyoyin Tafiyar Da Gamin Gambizar Sha’awa (4)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan hanyoyin tafiyar da gamin gambizar sha’awa daga inda muka tsaya a makon jiya, da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin.

Hanya Ta 5: Uwargida Ta Zama Cikakkiyar Mace:

Ga duk Uwargidan da take son samun nasara da farin ciki a gidan aurenta, a duniyarta da kuma lahirarta, to dole sai ta zama cikakkiyar ’ya mace, ta hanyar bankado da dukkanin siffofi, halayya da dabi’un macentaka da Allah SWT Ya gina jiki da ruhin ’ya mace da su. In Uwargida ta rika jin tana da wani nakasu ta fannin cikar macentakarta, to wannan zai dakusar mata da sha’awarta, mace ta fi jin sha’wa in ta rika jin ita cikakkiyar mace ce ta ko’ina, shi ya sa za ka ga mazan da suka gane wannan sirri suna yawan amfani da hikimomin macentakar matansu kusan a kowane lokaci.

Kowace mace, akwai wata irin baiwa ta musamman da Allah SWT Ya yi mata, matsalar yawancinmu ba mu san irin baiwar tamu ba, balle mu san yadda za mu sarrafata har ta amfanar da rayuwar aurenmu. Don haka yana da kyau Uwargida ta yi kokari ta fahimci kanta da yanayin halayyar ta, domin ta san yadda za ta rika sarrafa hikimomin macentakarta don samun babbar nasarar rayuwar aure.

Ado da kwalliya muhimmai ne daga cikin dabi’un jinsin ’ya mace da yin su ke rayar da sha’awarta, don haka yana da matukar alfanu ga Uwargida ta kasance kodayaushe cikin kwalliya, ba wai lallai sai lokacin tarbar maigida ba, har ma da lokacin gabatar da aikace-aikacen gida, ya kasance kodayaushe ta yi kwalliyarta daidai gwargwado, da ’yan kunne, sarka, warwaro da duk wani abin makalawa na kwalliya a jikinta, domin wannan zai kara fito wa uwargida da kwarjinin macentakarta, wanda ya kan taimaka wajen ji da motso sha’awar ’ya mace, kuma ya samar mata da wadatacciyar wadatar zuci.

Misalan irin dabi’u da halayen cikakkiyar ’ya mace sun hada da: Tsabta; yawan ado da kwalliya; wayau, hikima da fasaha; yanga, kwarkwasa da jan aji, tausayi da hakuri; kirki, kyauta da kyautatawa; ladabi, biyayya da girmamawa; kwantar da kai ga Maigida; fara’a, iya magana da sarrafa lafazi daidai da yanayi, da sauran su.

Akwai wasu mata da suka yi fice, duniya ta san da su saboda iya amfani da hikimomi da fasahohin macentakarsu; yana da kyau ga uwargida ta karanci tarihin wadannan mata, sai ta riki irin yadda suka yi rayuwarsu har suka kai ga matsayin da suka kai don ita ma ta rika aiwatar da haka don samun nasarar rayuwar aurenta.

Misalin Nana Khadijah RA, duk wanda ya san tarihinta ya san mace ce fasiha, mai tsananin hangen nesa, mai kyauta, mai kyautatawa, ga tauhidi da saurin fahimtar gaskiya, ga iya magana, ga kuma iya tafiyar da miji, tausayinsa, kwantar masa da hankali da taimakonsa.

Haka ma Ummuna Aisha RA, Mace mai ilmi, mai hikimar zama da miji da nuna masa so da kauna, ta yadda ko fushi ta ke da shi baya taba ganewa sai ta irin yanayin rantsuwar ta kawai!

Nana Asiya, RA, mace mai dabara, karfin hali da jarumta, yi la’akari da karfin mulki irin na fir’auna, da kuma yadda ta yi ta tafiyar da shi cikin wayo da hikima irin ta ’ya mace, in za ta yi masa magana sai ta zabi kalmomin da suka dace ta yadda da ya ji bai iya musa mata sai dai ya yi abin da take so.

Daga cikin sauran mata kuma akwai Sarauniya Cleopatra, wacce tarihi ya nuna ta kan yi amfani da kyawunta, iya caba ado da hikimomin nuna kauna wajen yaudarar manyan masu mulki na lokacin irin su Caesar har su fada cikin kogin kaunarta.

Sannan ga uwargida mai matsalar rashin cimma biyan bukatar sha’awa, to dole sai ta cire kunya ta sanar da maigida irin abubuwan da take ganin yin su gareta zai taimaka, saboda dai ita ke da jikinta, ita ta fi sanin irin abin da take ji, ba yadda za a yi maigida ya san abin da ya yi mata da wanda bai mata ba in ba gaya masa ta yi ba, sai dai ya yi ta lalube cikin duhu. Kunya na da wajenta cikin rayuwar aure, kamar kunyar gaya ma maigida bakar magana komai bacin rai saboda nauyinsa da ake ji, to irin wannan kunyar ta fi alfanu.

Sai sati na g ba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos