Hanyoyin tafiyar da Gamin Gambizar Sha’awa (8)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa  cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani a kan hanyoyin tafiyar da Gamin Gambizar Sha’awa daga inda muka tsaya a makon jiya. Da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga dukan masu bukatarsa […]

Hanyoyin tafiyar da Gamin Gambizar Sha’awa (8)
Hanyoyin tafiyar da Gamin Gambizar Sha’awa (8)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa  cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani a kan hanyoyin tafiyar da Gamin Gambizar Sha’awa daga inda muka tsaya a makon jiya. Da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga dukan masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin:

Hakukuwa Masu Inganta Ma’aikatar Sha’awa: Ga bayani kan wasu hakukuwa da bincike ya tabbatar suna taimakawa ga inganta lafiyar sha’awa kuma ba su da wata babbar illa ga lafiyar jikin dan Adam, sai dai a kula, dukan hakukuwan nan da zan zano, kada a hada shansu tare da wani magani, na gargajiya ko na zamani.

 

Karara (ko Sansoni): Allah (SWT) Ya albakaci ’ya’yan wannan bishiya da yalwar wani sinadari mai alfanu mai suna L-dopa, wanda in ya shiga cikin jini za a sarrafa shi zuwa sinadarin dopamine wanda ke da matukar alfanu ga gudanuwar ma’aikatar hankali musamman ta fannin shauki da motsin jijiyoyi, muhimman bangarori na ibadar aure. Haka sinadaran  ’ya’yan karara na kara karfin sha’awa da inganta ibadar aure. Ana iya dafa shi a ci kamar yadda ake dafa wake ko a gasa irin gashin da ake wa gyada, amma sai an kula  wajen amfani da shi, domin danyen shi na dauke da guba wacce ke iya haifar da lahani ga lafiyar jiki da kwakwalwa, sai an dafa shi akalla sau uku zuwa biyar ana sauya ruwa kafin a ci, in za a gasa ne kuma sai an wanke shi sosai ya bushe kafin a gasa.

Tsidau (ko Hana-Takama; Sesigi; Kayar Gobirawa): Amfani da wannan hakki yana matukar inganta lafiyar sha’awa da ma lafiyar jikin dan Adam gaba daya. Tsidau Yana dauke da sinadaran Saponins wadanda kasancewarsu cikin jini kan jawo bayyanar sinadarin Protodioscin wanda ke kara yawan sinadarin sha’awa cikin jini, ya buda hanyoyin jinin ma’aikatar sha’awa kuma ya jawo bayyanar sinadarai masu alfanu ga tabbatuwar sha’awa cikin jini. A iya zuba nikakken ganyen wannan haki cikin madara ko nono a sha.

Karamar Anta: Na dauke da sinadarai masu inganta ’ya’yan halittar da namiji da inganta motsinsu da kuma inganta lafiyar ruwan da ke dauke da su. Haka kuma sinadaran cikinta na matukar inganta lafiyar sha’awa ga  maza da mata. Ganye, ’ya’ya da saiwar wannan itaciya duk ana amfani da su wajen inganta lafiyar sha’awa da ta jiki duka.

Bakin Gagai: An dade ana amfani da shi a Kasar Hausa wajen maganin sanyin gaba ga maza, rashin haihuwa da karin sha’awa. Kuma binciken masana kimiyya ya tabbatar da alfanun wannan bishiya wajen kara yawan sinadarin testosterone cikin jini, da kuma kara lafiyar ma’aikatar sha’awa gaba daya ba tare da haifar da wata sananniyar matsala ba ga lafiyar jiki. Sai dai masana kimiyya a jikin bera kadai suka yi wannan gwaji har yanzu ba su yi shi ga dan Adam ba, amma kuma a hakan ya shiga kasuwar duniya har an sarrafa shi zuwa magani na zamani da za a iya hadiya; kuma da yawan masu amfani da shi na gamsuwa da ingancin aikinsa ga karin karsashi da kuzarin sha’awa da inganta lafiyar jiki duka.

Yohimbe: Kaucin wannan bishiya ya yi suna kwarai a fagen karin sha’awa da magance matsalar sanyin gaba na maza, sai dai yawanci an fi samunsa a Kudancin kasar nan, kamar jihohin Legas da Oyo. Ana jika nikakken kaucin a sha da ruwa ko madara. Yakan haifar da ’yan matsaloli kadan ga lafiyar jiki musamman in aka wuce ka’ida wajen amfani da shi.

Sauran hakukuwa da itatuwan da ake amfani da su wajen inganta lafiyar sha’awa sun hada da Ka- Fi-Malam; Ka-Fi-Boka (ko Farin -Gamo); Ka-Fi-Amarya; Ka-Fi Nama Zaki; Nonon Kurciya; Dafara; Namijin Tsada da sauransu. Ba wani cikakken bayani ko wani kwakkwaran binciken masana kimiyya game da su da ka iya tantance sinadaran da ke cikinsu don a tabbatar ba za su yi illa ga lafiyar jiki ba. Don haka akwai hadari sosai cikin shan irin wadannan hakukuwa ba bisa ka’ida ba.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe.