Hanyoyin tsabtace hannuwa daga kwayoyin cuta

Cikakken bayani kan hanyoyin tsaftace hannuwa daga kwayoyin cuta.

Hanyoyin tsabtace hannuwa daga kwayoyin cuta

Akowace shekara ranar 15 ga watan Oktoba ita ce ranar da hukumomin lafiya na kasashen duniya suka ware domin tunatarwa da fadakarwa da koyar da wanke hannuwa.

Sun sa wannan rana dab da makon yaki da kwayoyin cuta, wanda zai fara daga ranar Asabar.

Wanke hannuwa yana nufin tsabtace su daga kwayoyin cututtuka.

Mun sha ambata wa jama’a cewa a rika yawan wanke ko tsabtace hannuwa da ruwa da sabulu, ko da ruwa da toka, ko da man sanitaiza, amma ba a taba daukar lokaci an bi ita kanta hanyar wanke hannuwan sukutum an yi magana a kanta ba, wanda shi ne ginshikin tsabtace hannuwan.

A wannan lokaci da ake fama da annoba wadda kwayar cuta take yadawa, mutane da dama za su rika ganin ana ajiye bokitai ko tankuna masu famfo a gaban ma’aikatu da kasuwanni domin tsabtace hannuwa, a wasu wuraren ma har da man sanitaiza, inda za su ce ko dai ka wanke hannuwanka tas ko kuma ka shafa man kafin ka shigar musu haraba.

To yaya ake wanke hannuwa da ruwa da sabulu ko da man sanitaiza?

Akwai matakai 10 wadanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gindaya wadanda sai an bi su ne hannuwa suka zamo tsabtatattu. Wadannan matakan kuwa su ne:

  1. A kunna famfo a jika hannuwa da ruwa
  2. A shafa ko matsa sabulu idan na ruwa ne, ko taba toka ko yashi
  3. A murza tafin hannuwa
  4. A tsettsefe ’yan yatsu ta ciki
  5. A tsettsefe ’yan yatsu ta baya
  6. A makala yatsu su yi ankwa da juna don murza farata
  7. A wanke babbar yatsa ta dama sannan ta hagu
  8. A busar da hannuwan da tsabtataccen tawul ko mayanin tishu
  9. A kashe famfon da mayanin tishun ba da tsabtataccen hannun ba.

– Yadda ake tsabtace hannuwa da sanitaiza –

Idan man sanitaiza ne za a yi amfani da shi mataki na 2 ne kawai zuwa na tara, wato ba kunna ruwa, ba kashe ruwa.

Busar da hannuwa kuma a iska ake busarwa idan da man sanitaiza ne, ba da mayani ba.

An fi son amfani da man sanitaiza ba ruwa ba a mafiya yawan lokuta saboda shi ya fi kashe kwayoyin cuta.

– Lokacin da aka fi son amfani da ruwa –

Akwai kuma lokutan da aka fi so a yi amfani da ruwa ba man sanitaiza ba.

Misali idan an taba dauda wadda a ido ana gani kuru-kuru, kamar cabi ko tabo, ka ga ai man sanitaiza ba zai yi aiki ba, sai dai ruwa da sabulu.

Lokutan wanke hannu

Ban da lokutan shiga harabobin ma’aikatu, lokutan da aka fi so mutum ya rika yin wannan a kullum su ne;

  1. Idan daga bayan gida
  2. Bayan an canja wa yara nafkin
  3. Bayan an taba shara ko bola
  4. Bayan an yi atishawa ko tari a cikin hannuwa ko bayan fyace hanci da hannuwa
  5. Kafin cin abinci
  6. Bayan an taba marar lafiya, kamar mai amai da gudawa
  7. Kafin a wanke wa wani ciwo ko rauni da bayan an gama
  8. Bayan an je gona, an taba dabba ko sinadaran kemikal kamar taki ko maganin kwari.

Dokta Auwal Bala I-mel: [email protected] Sakon Tes: 08029013880