Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa

Wata hanya mai hatsari ita ce ’Yantumaki–Dutsinma, wadda direbobi suke yi wa laƙabi da “Ka bi ta da addu’a.” Yawancin matafiya a hanyar suna bayyana ta a matsayin tarko na mutuwa.

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa

Masu garkuwa da mutane

“Sanin kowa ne a halin yanzu gwamnati ta yi ƙoƙarin buɗe dukkan kasuwanninmu, kuma a yau babu hanyar da ba a bi a faɗin Jihar Katsina. Fatanmu shi ne, abubuwan da suka rage mu dage da addu’a da ƙoƙarin gano waɗanda ke yi mana zagon ƙasa ta fuskar tsaro domin sanar da gwamnati a lokacin da ya dace a ɗauki matakin da ya dace.”

Waɗannan su ne kalaman Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal Joɓe, a jawabinsa a lokacin da ya wakilci Gwamna Dikko Raɗɗa a ranar Hawan Sarki a shagalin bikin Babbar Sallah da aka yi a satin da ya gabata.

Sai dai kalmansa na cewa “…babu hanyar da ba a bi a faɗin Jihar Katsina” ta kawo ce-ceku-ce, inda wasu ke ganin furucin tamkar gwamnatin ba ta san abin da ke faruwa a wasu sassan jihar ba, yayin da wasu ke ganin ya yi lakaman ne don kwantar wa da jama’a hankali, musamman alaƙanta jawabin da buɗe kasuwanni da aka yi saɓanin baya.

Ba da jimawa ba ne kuma, aka samu rahoton cewa ’yan bindiga sun tare wata hanya a jihar, inda suka yi garkuwa da Manjo-Janar Rabe Abubakar Batsari (Ritaya), tsohon Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya.

A kan haka ne, Aminiya ta ya yi ƙoƙarin gano aihinin halin da manyan hanyoyin shiga jihar, wadda ke fama da hare-haren ’yan ta’adda masu yin garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa.

A can baya a lokacin da hare-haren ’yan bindiga suka yi ƙamari a yankunan ƙananan hukumomin 18-19, dole ta sa direbobi da sauran matafiya suka daina bin wasu hanyoyi a jihar saboda tsohon harin ’yan ta’addan.

A lokacin baya, hukumomi da ƙungiyoyi musamman na direbobi sun yi gargaɗin barin bin irin waɗannan hanyoyi masu haɗari, kamar hanyar Katsina zuwa Batsari ko Jibiya ko zuwa Ƙanƙara har zuwa Faskari ko Bakori.

Haka ma hanyar Ɗandume zuwa Birnin Gwari ko Sabuwa da hanyar Batsari zuwa Jibiya ko Safana ko Ɗanmusa, duk sai dai a bi su cikin faɗuwar gaba ko kasada.

 

Hanyoyi mafiya haɗari zuwa Katsina

Aminiya ta ruwaito cewa hanyoyi mafiya haɗari a Jihar Katsina saboda hare-haren ’yan bindiga sun haɗa da hanyar Marabar Musawa– Matazu–Kafin Soli–Charanchi, Katsina–Dutsinma, hanyar Ƙanƙara–Marabar Ƙankara, Funtua–Tsafe–Gusau, da kuma babbar hanyar Jibia–Sakkwato.

Sauran sun haɗa da hanyar Marabar Sheme–Ƙanƙara, Marabar Ƙankara–Ƙanƙara– Dutsinma, da hanyar Katsina– Kankia–Gidan Mutum Ɗaya– Dayi–Malumfashi.

Rahotanni sun ya nuna cewa direbobi sun daina bi ta hanyar Marabar Musawa–Matazu– Kafin Soli–Charanchi saboda yawan hare-haren ’yan bindiga da ke amfani da dazuzzuka da yawan ciyayi wajen kai harehare.

Wannan hanya ta haɗa Katsina da Kaduna, Funtua, Malumfashi har ma da wasu sassan Jihar Kano, ciki har da Ƙaramar Hukumar Gwarzo.

Wani mazaunin garin Musawa, Malam Yusuf Alasan, ya shaida wa wakilinmu cewa kusan shekaru uku ne nan da direbobi suka ƙaurace wa hanyar.

“Za ka iya yin tafiyar minti 40 ba tare da ka haɗu da wata mota ba. Wannan ya nuna yadda aka bar hanyar. Na yi imani cewa tsohon sojan da aka yi garkuwa da shi kwanan nan bai san halin tsaron da ake ciki ba a hanyar,” in ji shi.

Malam Yusuf ya ce ’yan bindiga suna amfani da dazuzzukan yankin wurin kai hare-hare a duk lokaci cikin dare ko yini.

“Ba da jimawa ba, ’yan bindiga sun bi ta cikin wannan gari da wani wanda suka yi garkuwa da shi. Suna kan babura uku, kowane babur ɗauke da mutane uku. An rufe kan wanda aka yi garkuwa da shi da baƙin ƙyalle kuma hannuwansa an ɗaure. Dukkansu suna ɗauke da bindigogi,” in ji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa yawancin matafiya daga Abuja da Kaduna yanzu suna shiga Katsina ne ta Kano, wasu kuma ta Daura domin guje wa barazanar ’yan bindiga.

 

Tsananin hare-hare a hanyoyin Katsina

Hanyar Katsina-DutsinmaMarabar Ƙankara tana da haɗari musamman tsakanin Dutsinma da ’Yargoje, yayin da hanyar Katsina-KankiaGidan Mutum Ɗaya-Dayi-Malumfashi ta fi haɗari tsakanin Kankia da Dayi.

Hanyar Ƙanƙara-Ruwan Godiya-Faskari ma ’yan bindiga sun addabe ta, duk da cewa ita ce hanya mafi gajarta tsakanin Ƙanƙara da Faskari.

Hanyar ta dangana zuwa Tsafe da Gusau, da tsawon kilomita 15 zuwa 20, amma yanzu saboda rashin tsaro, direbobi sun koma bi ta hanyar Ƙanƙara-Funtua-Faskari mai tsawon fiye da kilomita 50.

Wata hanya mai hatsari ita ce ’Yantumaki–Dutsinma, wadda direbobi suke yi wa laƙabi da “Ka bi ta da addu’a.” Yawancin matafiya a hanyar suna bayyana ta a matsayin tarko na mutuwa.

Haka kuma, hanyar Kankara–Mabai–Ruwan Godiya–Faskari an guje ta, yawanci sai jami’an tsaro masu makamai ne kawai ke bin ta.

Babbar hanyar Jibia– Sakkwato, wadda ke haɗa jihohin Katsina da Sakkwato, ita ma ta yi ƙaurin suna da hareharen ’yan bindiga.

Ko da yake ita ce mafi sauri tsakanin Jibia da Sakwato, amma hare-haren sun sa direbobi da dama sun guje ta tsawon shekaru.

Mazauna sun ce an yi garkuwa da fasinjoji da dama ko an kashe su a kan hanyar.

Hanyar Marabar Sheme–Ƙanƙara, wata muhimmiyar hanya da ke haɗa Ƙanƙara da Tsafe da Gusau, amma ma an bar ta.

Direbobi da ke zuwa Gusau ta Ƙanƙara yanzu suna bi ta Funtua, wanda hakan ke ƙara kusan awa ɗaya a tafiyarsu.

Ga yawancin mazauna da matafiya, waɗannan hanyoyi sun zama alamu na tsanantar matsalar tsaro da ke addabar Jihar Katsina da yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya.

Sanadiyar rashin bin hanyoyin ya sa har ta kai fagen rufe wasu kasuwannin jihar musamman masu ci satisati. An rufe babbar Kasuwar Charanci da Kasuwar Jibiya da Kasuwar Mai’aduwa da sauran manyan kasuwannin jihar ta dalilin wancan rashin tsaro.

Daga baya a hankali abubuwa suka fara sauƙi har aka koma bin waɗannan hanyoyi. An ƙara samun sauƙi bayan yin sulhu da su jama’ar yankunan da matsalar tsaron ta fi shafa suka yi da ’yan bindigar.

Wanna ya faru ne bayan tun da farko bayan hawan Gwamna Dikko Umar Raɗɗa bayan bisa mulki ya sanar da cewar babu shi ba sulhu da ’yan ta’addar sai fa in su ne suka tuba da kansu kuma suka miƙa wuya.

Ana cikin wannan zama na sulhu da fara ci gaba da walwala, kwatsam sai rahotanni suka fara fitowa daga yankin Ƙanƙara na cewa, wasu ’yan bindigar sun dawo suna tare hanya tare da yin garkuwa da matafiya, musamman hanyar Guga da Sheme. Sai kuma wajen yankin ƙaramar hukumar Dutsinma.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya bayyana cewa, a yanzu abin ya fi ɓaci a kan hanyar Katsina zuwa Matazu har Musawa.

Rahotanni sun bayya cewa wani tubabben ɗan ta’addan da ya tayar da tuba, mai suna Kacalla Muhammadu Fulani ne tare da yaransa suka addabi wannan hanya, kuma ya faɗaɗa ayyukan ta’addancin nasa har zuwa kan hanyar da ta taso daga Malunfashi zuwa Gidan Mutun Ɗaya. Kachalla Fulani ya kuma addabi al’ummomin garin Sayaya da Matazu da sauran ƙauyukan yankin har ya zuwa yankin Rimaye da Kankiya.

 

Yadda aka yi garkuwa da Janar Rabe

A ranar Asabar da ta gabata ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya, ManjoJanar Rabe Abubakar Batsari (ritaya) tare a matarsa a hanyar Marabar Musawa-Kafin Soli da ke Karamar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina.

Shaidu sun bayyana cewa maharan sun fito daga cikin daji ne suka tare hanyar, inda suka bude wa motar Janar ɗin wuta a lokacin da yake wucewa a hanyar, wadda matafiya da dama suka kaurace mata saboda yawan hare-haren ’yan ta’adda.

Sun ce dole ta tsaya, suka yi awon gaba da shi da matarsa zuwa cikin jeji, suka harbi direbansa, amma suka yi watsi da shi.

A ranar Litinin jagoran ’yan bindiga, Kachallah Muhammad, ya buƙaci gwamnati ta sako ’yan uwansa da ke hannunta a matsayin sharaɗin sakin Janar Rabe.

Wani babban jami’in ƙaramar hukumar Batsari da ya yi bayani a sirrance saboda dalilan tsaro ya shaida wa wakilinmu cewa “Na yi magana Janar Rabe ta hannun Kachalla Muhammad kuma ya tabbatar mini cewa shi da mai dakinsa suna nan lafiya,” yana mai shaida wa ’yan uwa cewa masu garkuwa da su, suna kula da su, lamarin da ya rage fargabar da al’umma ke ciki game da garkuwar.

Jami’in ya bayyana cewa a yayin tattaunawar tasu, Kachalla Muhammad ya ba cewa abin da yake bukata shi ne jami’an tsaro su suka wasu ’yan uwansu da ke tsare a hannunsu.

“Ya ce yana so a sako ’yan uwanda da ke hannun gwamnati ba tare da bata lokaci ba, kuma a shirye yake a koma teburin sasanci da shi domin samun zaman lafiya a yankin Karamar Hukumar Matazu da makwabtansu da yake da iko,” a cewar jami’in.

 

Wane ne Kacalla Fulani?

Muhammdu Fulani haifaffen yankin rugagen Fulanin da ke yammacin garin Matazu ne. Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban Ƙaramar Hukumar Matazu, Honarabul Shamsu ne ya nemi a yi sasanci da shi.

Ana zargin Fulani ya tayar da tubansa ne bisa zargin shugaban ƙararar hukumar da yi masa maƙarƙashiya da cin amana har aka kama danginsa, waɗanda ake zargi da ta’addanci, bayan an yi sulhun, tare ta barazanar halaka ciyaman ɗin.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta a ƙaramar hukumar ta ce, shugaban ƙaramar hukumar yakan ba wa Fulani kuɗaɗe kamar yadda takwarorinsa suke ba wa ’yan bindigar da aka yi sulhu da su a duk wata.

“An ce, rashin ci gaba da ba Fulani waɗannan kuɗaɗe ya harzuƙa shi ya tayar da wancan sulhu. Mun ji ma an ce ya gaya wa shugaban ƙaramar hukumar cewa duk ranar da suka yi arba sai ya kashe shi. Hakan aka yanke zaman, shi Honarabul garin na Matazu ya gagare shi, ya koma Katsina da zama. Harkokin mulki ma munji an ce, duk can ake yi,” in ji majiyar.

Wata majiyar kuma ta bayyana cewa, Fulani ya tayar da tuba ne bisa koken cewa jami’an tsaso sun ƙwace masa shanu 700 da tumaki 1,000, bayan kuma an kama masa wasu dabbobi, amma babu abin da gwamnati ta yi ma shi.

A dalilin haka ne ya tayar da tuba ya ci gaba da kai hare-haren a yankunan Matazu da Musawa da Marabar Ƙanƙara da Sayaya da Rinjin Idi da Mazoji A da B har zuwa yankin Sukuntuni, da Rimaye da Kankiya. Ana kuma zarign wannan ɗan ta’adda ne ke kai hare-haren har a yankin Jihar Kano.

 

Haɗarin hanyar Matazu

Wakilinmu ya ruwaito cewa a halin yanzu hanya mafi haɗari a Jihar Katsina ita ce hanyar da Musawa zuwa Matazu har zuwa Kafin Soli.

Wani direba da ya tsallake rijiya ta baya daga tarkon maharan a hanyar, Malam Muhammadu Direba, ya ce, abin ya fi ƙamari daga Kwanar Hanyar Sayaya zuwa Kafin Soli.

“Duk da babu wani babban daji a yankin sai dai yawan hanyoyin kurɗe, waɗanda ke shiga har zuwa yankin Faskari a shiga har zuwa yankin Zamfara,” in ji Malam

Muhammadu direba wanda ya bayyana cewa yana wucewa ta hanyar Sayaya ’yan bindiga suna na fitowa kan babura.

Har ila yau, ita kanta hanyar da ake bi wadda ke zuwa Gidan Mutun Ɗaya, a kan fuskanci wannan barazana.

Wani da aka zanta da shi ya ce, “Abin da ya fi ɗaure mani kai shi ne, sace wannan Manjo Janar Rabe Abubakar, duk kuwa da cewar akwai jami’an tsaron sojoji kusa da sakatariyar ta Matazu.

“Abu na biyu shi ne, a ce wai duk tulin jami’an tsaron leƙen asiri da neman bayanan sirrin da ake da su amma a ce, wai ɗan ta’adda za a riƙa bayanin shi wannan ManjoJanar bayanan fitowar shi tun daga garin Kaduna har zuwa Marabar Ƙanƙara, inda shi Fulani ya yi shirin ɗaukar shi idan ya zo wajen Gidan Mutun Ɗaya, amma sai shi Manjo ya canza hanya inda ya biyo ita wannan hanya ta Matazu ba tare da ya san abin da ke faruwa ba, kamar yadda wasu bayanan ke shigo mana.

“An ce jin an biyo wannan hanya ya sa shi Fulani ya kafa wancan tarko domin abin ya zo mashi da sauƙi,” in ji wani mazaunin garin Matazu da ya nemi a sakaya sunan saboda tsaro.

A yanzu dai batun tare hanya da hare-haren kisa za a iya cewa sun bar Arewaci da Yammacin babban birnin Jihar Katsina, sun koma daga Kudanci musamman hanyar Matazu zuwa Musawa da ta zamo wani babban tarkon mutuwa ko shiga hannun ’yan ta’addan da ke yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.