Har abada babu mai rushe sabbin masarautun Kano —Ganduje
Ganduje ya ce Allah Ba zai kawo wa gwamnan da zai rusa sabbin masarautun Kano ba
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce babu gwamnan jihar da zai zo ya rushe sabbin masarautu hudu da gwamnatinsa ta kafa.
Ganduje ya bayyana cewa Allah ba zai kawo gwamnan da zai rusa sabbin masarautun ba, wadanda ya bayyana a matsayin alamar cigaba da hadin kai da kuma zaman lafiyar Jihar Kano.
- JAMB: Talata sakamakon jarabawar 2023 zai fito
- Gwamnati za ta cefanar da Asibitin Fadar Shugaban Kasa
“Ina tabbatar muku babu abin da zai kawar da su da izinin Allah har zuwa karshen duniya.
“Mai niyyar rusa su kuma Allah Ba zai kawo shi jihar Kano ba, kuma muna tabbatar muku cewa an yi wadannan masarautu ne domin ku da kuma ci gabanku.
“Muna rokon Allah, ko mun bar mulki, Ya kare wadannan masarautu daga sharri,” in ji Ganduje.
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP ya kuma yi tsokaci kan sabbin masarautu hudu da Ganduje ya kafa, a matasyin abin da ya kamata Gwamnatin Abba Kabir Yusuf mai jiran gado ta duba.
Madugun Kwakwasiyyan ya yi tsokacin ne bayan ce-ce-ku-cen da ya karade kafofin sanda zumunta cewa gwamnatin Abba za ta dawo da Sarki Sanusi II kan kujerarsa kuma ta hade masa Masarautar Kano kamar yadda take kafin Ganduje ya tube shi.
Sanusi II wanda ke dasawa da Kwankwaso, ya yi ta samun takun saka ga Gwamnatin Ganduje, har daga karshe ta tube masa rawani.
Sai dai yayin jawabinsa a taron Ranar Ma’aikata a jihar, Ganduje ya ce, Allah Ba zai jarrabi Jihar Kano da gwamnan da zai rusa masarautun ba.
Ya bayyana wa taron ma’aikatan cewa “Duk wanda ya je hedikwatar wadannan masarautu zai shaida cewa mun kawo musu cigaba.
“Wadannan masarautu an samar da su ne saboda hadin kai da cigaba da tarihi da kuma farfado da daraja da al’addu da kuma wadannan yankuna,” in ji shi.