Har matan gwamnoni nake wa lalle – Hindatu
Hindatu Muhammad Nura wata gurguwa ce da ta kware a sana’ar lalle wanda aka fi sani da sunan Dayis. A zantawarta da Aminiya ta bayyana yadda take gudanar da wannan sana’ar da nasarorin da ta samu, da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Ko za ki bayyana mana tarihinki a kaice?Hindatu: Sunana Hindatu […]
Hindatu Muhammad Nura wata gurguwa ce da ta kware a sana’ar lalle wanda aka fi sani da sunan Dayis. A zantawarta da Aminiya ta bayyana yadda take gudanar da wannan sana’ar da nasarorin da ta samu, da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ko za ki bayyana mana tarihinki a kaice?
Hindatu: Sunana Hindatu Muhammad Nura, ina zaune ne a Unguwar Bolari Filin kwallo kusa da Masallacin Juma’a na Izala da ke Jihar Gombe.
Aminiya: A wane wuri kika koyi sana’ar lalle kuma tun yaushe kike wannan sana’ar?
Hindatu: Ba wanda ya koya mini daga Allah ne kawai kuma shi ya bani ikon kirkiro salo daban-daban na lalle, kuma da haka har nake koyar da wasu. Akalla na kai shekara 10 ina wannan sana’ar tun ba a san ni ba har yanzu ya zama a fadin jihar nan babu kamata. Wannan sana’ar ta rufa mini asiri domin kullum bana rasa abin biyan bukata ta.
Aminiya: Kimanin mutane nawa kika koya wa wannan sana’ar?
Hindatu: Eh na koya wa mutum biyar wannan sana’ar kuma dukkansu kannena ne wadanda yanzu haka duka suna gidajen mazansu suna kuma taimakawa kansu da wannan sana’ar.
Aminiya: Wadanne irin mutane ne kike wa aiki?
Hindatu: A gaskiya na yiwa manyan mata masu mutunci sosai, inda wasu za su biyaka daidai kudin aikinka wasu kuma za su biyaka fiye da abin da ya kamata su biya kuma gaskiya na yi wa har matan gwamnoni, a lokacin mulkin gwamna Danjuma Goje, ina yiwa Amaryarsa Hajiya Munnira Goje, kanwata da na koya wa kuma ita take yi wa uwargidansa Hajiya Yelwa Goje. A lokacin da gwamna Dankwambo ya ci zabe na yi wa matarsa =Hajiya Adama dankwambo a safiyar ranar da aka rantsar da shi.
Aminiya: Ta wace hanya suka sami labarinki har ma suka bukaci aikinki?
Hindatu: Tambaya suke yi a nemo musu wacce tafi iya Dayis bayan sun gani a wajen wasu dana yi wa. Ta haka wata rana kawai sai na ga anzo gida, aka dauke ni ba shiri aka tafi da ni naje gidajensu na yi musu kuma gaskiya ina musu da kyau bana ha’inci shi ya sa.
Aminiya: Kamar nawa ake biyanki ladan aiki?
Hindatu: Ba yadda ba na karba daga naira dari biyar zuwa dubu daya har dubu daya da dari biyar zuwa sama. Ina karbar kudin ne bisa ga karfin mutum saboda kowa a sana’arsa zai taimaki wani saboda ba ka san kai ma waye zai taimakeka nan gaba ba.
Aminiya: Kamar matan manyan nawa kike karba a wajensu?
Hindatu: Ai na gaya maka babu yadda bana karba su kuma manyan matan nan ba biya suke yi ba kyauta kawai suke bayarwa. Kamar amare kuma idan na ga amarya tazo ba ta da kudi ina iya mata na naira dubu biyu ko fiye da haka a naira dari biyar ko dubu daya saboda na ga aure za su yi kuma suna da dawainiya.
Aminiya: Wane irin rufin asiri kika samu ta dalilin wannan sana’ar?
Hindatu: Alhamdulillahi na samu rufin asirin da komai nake nema na rayuwata ina iya yi wa kai na duk da cewa iyayena suna da rufin asiri daidai gwargwado a haka ma wata rana ina ba su wasu yan kudi saboda neman albarkansu.
Aminiya: Akwai kasashe ko garuruwa da kika taba zuwa ta dalilin sana’ar?
Hindatu: Iya kacina Najeriya ban taba fita wata kasar waje ba amma ana zuwa a dauke ni daga jihohi irinsu Kaduna, Kano, Abuja da kuma Jos. Har ila yau, a nan Jihar Gombe kuma naje kusan duka kananan hukumomin nan 11, na yi wa mata lalle.
Aminiya: Wane kira kike da shi ga masu nakasa da suke bara?
Hindatu: Ni ina ganin baran nan da irina masu nakasa ke yi kamar zubar da mutunci ne domin ba laile ba ne idan mutum yana baran ya samu biyan bukata. Kamata ya yi ace mutum ya samu sana’ar da zai yi don ya dogara da kansa har wasu ma su zo karkashinsa, kamar ni ai saboda sana’ar da nake yi ka ga babu mai wulakanta ni.
Aminiya: Ga shi kina karatu a jami’a da wannan sana’ar kike daukar nauyin karatun ki?
Hindatu: Eh gaskiya da iyayen amma tsohon Shugaban Jami’ar Jihar Gombe ne, Farfesa Abdullahi Mahdi, yake biya mini kudin makaranta har da kudin kashewa yake ba ni sannan kuma ina yi wa kai duk abin da nake so ta wannan sana’ar. Kuma ina karatu ne a fannin nazarin darussan adddinin Musulunci wato Islamic Studies
Aminiya: Ki na da wani kira ga gwamnati?
Hindatu: Gaskiya ina kira ga gwamnati da ta taimaka ta samar mana da katafaren waje don fadada sana’armu, inda za mu kara daukar wasu mu koya musu sana’ar su samu hanyar dogara da kansu don rage zaman banza da yawon bara a gari.