Har yanzu akwai matsalar hauhawar farashi a Najeriya — Bankin Duniya

Bankin ya ba da shawarar nemo hanyoyin da suka dace domin hana hauhawar farashin kayan masarufi.

Har yanzu akwai matsalar hauhawar farashi a Najeriya — Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa tattalin arziƙin Najeriya zai bunƙasa a farkon shekarar 2026, sai dai hauhawar farashin kayayyaki da ƙarin kuɗin man fetur na ci gaba da rage kuɗin shiga da al’umma ke samu.

Babban masanin tattalin arziƙi na bankin a Najeriya, Fiseha Haile ne, ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a Abuja.

Ya bayyana cewa harkokin kasuwanci na samun ci gaba, amma hauhawar farashi na ci gaba da kasancewa babbar matsala.

Duk da cewa hauhawar farashin ta ragu zuwa kusan kashi 15 a watan Fabrairu, idan aka kwatanta da kashi 33 a ƙarshen shekarar 2024, adadin yana da yawa idan aka kwatanta da sauran ƙasashe.

Lamarin ya ƙara tsananta sakamakon yaƙin Iran da Isra’ila da Amurka, wanda ya janyo tashin farashin ɗanyen mai da kashi 50.

Wannan ya haifar da tsadar sufuri, abinci da sauran kayayyakin masarufi.

Bankin ya yi hasashen cewa tattalin arziƙin Najeriya zai bunƙasa da kusan kashi 4.2 a shekarar 2026.

Haka kuma, ya shawarci gwamnati da ta adana ƙarin kuɗaɗen da ake samu daga man fetur, ta ƙarfafa manufofin kuɗi, sannan ta guji bayar da tallafi domin daƙile hauhawar farashi.

A nasa ɓangaren, Mathew Verghis, ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashin na ci gaba da jefa magidanta cikin ƙunci.

Ya jaddada cewa rage hauhawar farashi ita ce hanya mafi sauri da za ta sa al’umma su fara morar sauye-sauyen tattalin arziƙi.

Haka kuma, rahoton ya nuna wasu matsalolin zamantakewa, inda ya bayyana cewa har yanzu ana samun mace-macen yara kafin su kai shekaru biyar.

Sannan ya koka kan yadda da yawa ke yin aiki da ke da ƙarancin albashi.

Rahoton ya nuna cewa kusan kashi 10.5 ne kawai na matan da ke aiki ke samun ayyukan yi masu ɗorewa.

Har ila yau, Bankin Duniya ya jaddada buƙatar inganta wutar lantarki, samar da kyakkyawan shugabanci, da kuma tallafa wa mata domin ɗorewar bunƙasar tattalin arziƙi da inganta rayuwar al’umma a Najeriya.