Har yanzu alhazan da gini ya fada musu a Ka’aba ba a biya su diyya ba

Wadansu daga cikin alhazan Najeriya da hadarin da aka yi a shekarar 2015 a Masallacin Ka’aba ya rutsa da su sun koka kan cewa har yanzu ba a biya su kudin diyya da kasar Saudiyya ta bayar a ba su ba. A cewarsu shekara shida ke nan da aukuwar lamarin ba su ji komai ba […]

Har yanzu alhazan da gini ya fada musu a Ka’aba ba a biya su diyya ba

Wadansu daga cikin alhazan Najeriya da hadarin da aka yi a shekarar 2015 a Masallacin Ka’aba ya rutsa da su sun koka kan cewa har yanzu ba a biya su kudin diyya da kasar Saudiyya ta bayar a ba su ba.

A cewarsu shekara shida ke nan da aukuwar lamarin ba su ji komai ba daga Hukumar Hajji ta Kasa dangane da kudadensu.

Idan za a tuna a ranar 11 ga Satumban 2015 ce wani karfe ya fado a kan alhazan da suke cikin masallacin lokacin da suke gudanar da ibada wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwar da yawa daga cikinsu, wadansu kuma suka samu raunuka.

Akalla alhazan Najeriya shida ne suka rasu wadanda suka fito daga jihohin Gombe da Katsina da Kaduna sannan wadansu suka samu raunuka.

Hukumomin Saudiya sun fitar da diyyar dukkan wadanda suka samu raunuka ko suka rasu a sakamakon wannan hadari domin biyan su.

A cewar sanarwar Fadar Sarkin Saudiyyar duk wanda ya samu rauni za a biya shi diyyar Naira miliyan 26.5 sannan wanda ya rasu iyalinsa za su samu diyyar Naira miliyan 53.1.

Dan uwan marigayi Shu’aibu Adamu dan Karamar Hukumar Kubau a Jihar Kaduna wanda ya rasu a hadari da kuma Ibrahim Sani wanda ya ce shi rauni ya samu a hadarin, sun koka kan cewa ba a biya su hakkokinsu ba sannan ba su da bayanin a kan yaushe za a biya.

Yayan marigayi Zubairu Adamu da Ibrahim Sani ne suka sanar da ’yan jarida haka jim kadan bayan sun kai wasikar kokensu gidan Gwamnatin Jihar Kaduna domin neman Gwamna Nasir El-Rufa’i ya taimaka ya sa baki a biya su hakkokinsu.

A cewar Zubairu, dan uwansa, marigayi Shu’aibu, ya bar mata biyu da marayu goma wadanda har yanzu suna zaman jiran diyyar mahaifinsu.

“Shekara shida ke nan da aukuwar lamarin a Masallacin Harami kuma babu wanda ya ce da iyalansa komai dangane da diyyar tasa, kuma duk kokarin da muka yi na bin hakkokinsu abin ya ci tura don haka muke neman Gwamnan Jihar Kaduna ya taimaka mana a karbo hakkin marigayin,” inji shi.

Ya kara da cewa suna da labarin Gwamnatin Saudiya ta ce ta biya Najeriya wadannan kudade amma har yanzu su ba su samu diyyar ba.

Shi ma Ibrahim Sani wanda ya ce shi rauni ya ji a lokacin hadarin cewa ya yi sun rubuta takardu zuwa Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) da ke Abuja da ta Jihar Kaduna a kan neman karin bayani amma ba a ba su gamsasshiyar amsa ba dangane da lokacin biyan wannan diyya.

Da Aminiya ta tuntubi Mukaddashin Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna, Hajiya Hannatu Zailani, ta tabbatar da cewa a shekarar 2018 Hukumar Hajji ta Kasa ta aiko musu da takardar kudin mamacin Shu’aibu Adamu dauke da sunansa maimakon a rubuta sunan magajinsa tunda babu yadda za a yi mamaci ya karbi kudi a banki.

“Hakan ya sa muka mayar wa NAHCON domin a gyara sunan kuma suka ce za su mayar Saudiyya domin a gyara a can amma sai aka fara cutar COVID-19 da ta hana yin tafiya.

“A yanzu ne kofa ta bude don haka yanzu komai na a hannun NAHCON mu ma jira muke yi mu ji daga NAHCON,” inji ta.

Dangane da batun Alhaji Ibrahim Sani wanda ya ce ya ji rauni sai ta ce su a Hukumar Alhazai ta Jihar ba su san da zancensa ba.