Har yanzu ba bu dan takarar Gwamna na APGA a Imo- Onyeagucha
Dan takarar Gwamna daga jam’iyyar APGA a jihar Imo Uche Onyeagucha, ya ce jam’iyyar har yanzu ba ta fitar da dan takarar gwamna a zaben 2019 ba. Ya ce, saboda jam’iyyar ba ta yi zaben fidda gwani ba, don fitar da dan takarar Gwamnan jihar kuma ya musanta rahoton Sanata Ifeanyi Araraume a matsayin zababban […]
Dan takarar Gwamna daga jam’iyyar APGA a jihar Imo Uche Onyeagucha, ya ce jam’iyyar har yanzu ba ta fitar da dan takarar gwamna a zaben 2019 ba.
Ya ce, saboda jam’iyyar ba ta yi zaben fidda gwani ba, don fitar da dan takarar Gwamnan jihar kuma ya musanta rahoton Sanata Ifeanyi Araraume a matsayin zababban dan takara da zai wakilci jam’iyyar.
Onyeagucha, ya bayyana hakan ne, a wata sanarawa da sakataran watsa labaransa Macdonald Enwere, ya fitar kuma ya karyata batun fitarsa daga APGA zuwa jam’iyyar PDP.