Har yanzu babu dan takarar Gwamnan Imo a APC -Ekechi
Wani babban jigo a jam’iyyar APC reshen jihar Imo Dakta Theodore Ekechi ya musanta rahoton da ake cewa an fitar da dan takarar gwamnan jihar, jam’iyyar a yanzu haka ba ta fitar da dan takarar neman Gwamnan ba a zaben 2019. Ekechi ya bayyana wa majiyarmu hakan ne a Owerri babban birnin jihar yau Talata. […]
APC
Wani babban jigo a jam’iyyar APC reshen jihar Imo Dakta Theodore Ekechi ya musanta rahoton da ake cewa an fitar da dan takarar gwamnan jihar, jam’iyyar a yanzu haka ba ta fitar da dan takarar neman Gwamnan ba a zaben 2019.
Ekechi ya bayyana wa majiyarmu hakan ne a Owerri babban birnin jihar yau Talata. Ya ce Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ne ya gaza tsara yadda za abi a cika wa’adin hukumar zabe wanda ya janyo tangarda a siyasar jihar Imo.