Har yanzu ba mu ga aikin kirki a Jihar Bauchi ba – Bababa
Shugaban kungiyar Masu Maganin Gargajiya ta Shiyyar Bauchi ta Kudu, Alhaji Gambo Abdullahi Bababa ya koka kan rashin ayyukan raya kasa a Jihar Bauchi, inda ya ce har yanzu babu wani aikin kirki da aka fara aka kammala kusan shekara uku na gwamnatin jihar. Alhaji Gambo Bababa ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa […]
Shugaban kungiyar Masu Maganin Gargajiya ta Shiyyar Bauchi ta Kudu, Alhaji Gambo Abdullahi Bababa ya koka kan rashin ayyukan raya kasa a Jihar Bauchi, inda ya ce har yanzu babu wani aikin kirki da aka fara aka kammala kusan shekara uku na gwamnatin jihar.
Alhaji Gambo Bababa ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Bauchi, inda ya ce, al’amura ba su tafiya daidai ne a jihar sakamakon yadda Gwamnan Jihar Alhaji Mohammed Abdullahi Abubakar ya zamo shi kadai ne ki mulkin jihar kuma bai cika zama ba. “Gwamna shi kadai yake mulki, a shekara uku bai zauna da kwamishinoni na rabin lokacin ba, sannan a matakan kananan hukumomi ba nadaddun shugabanni balle zababbu a kusan shekara biyu daga cikin uku na mulkinsa. Yaya za a yi ayyuka su gudana alhali kuma ba zama yake a jihar ba? Wannan ya sa duk ayyukan da gwamnatin ta bayar suke tafiyar hawainiya tunda babu mukarraban da za su tallafa wa Gwamnan wajen ganin an kammala su a kan lokaci,” inji Bababa.
“Jihar Bauchi jiha ce ta ma’aikata, Gwamna ya kama komai ya rike, shi ne Gwamna shi ne kwamishinoni shi ne ciyamomi, dole mu yi ta fama da talauci, domin sai ma’aikata na walwala mu ’yan kasuwa za mu yi, wannan ya jawo mana karayar jari, matasa suna ta gararamba. Kuma abin takaicin ’yan kore da ’yan ma’abba ba kunya ba tsoron Allah suna sayar da lahirarsu suna shiga kafafen watsa labarai suna cewa komai yana tafiya daidai, ko an yi aiki kaza da kaza, amma da za a turke su ba za su iya nuna ayyukan ba,” inji shi.
Shugaban ya ce babu yadda za a yi gwamnati ta yi tafiyar kirki idan ta kasance a hannun mutum guda shi kadai, sai ya yi kira ga Gwamna Abubakar ya sauya salon tafiyar da yake yi, domin wannan salo ne ya dada jefa jihar a cikin kuncin talauci.