Har yanzu ba mu ga danmu ba –Mahaifiyar Mai kusumbin da aka sace

Fiye da kwana 50 da sace matashin nan mai suna Mudassir Mai kusumbi da wasu mutane suka zo har cikin gidansu a Unguwar Bachirawa a birnin Kano suka sace shi, mahaifiyarsa ta ce har yanzu ba a gano shi ba. An rika yada rade-radin cewa Mudassir Mai kusumbi ya dawo a kwanakin baya, sai dai […]

Har yanzu ba mu ga danmu ba –Mahaifiyar Mai kusumbin da aka sace
Har yanzu ba mu ga danmu ba –Mahaifiyar Mai kusumbin da aka sace

Fiye da kwana 50 da sace matashin nan mai suna Mudassir Mai kusumbi da wasu mutane suka zo har cikin gidansu a Unguwar Bachirawa a birnin Kano suka sace shi, mahaifiyarsa ta ce har yanzu ba a gano shi ba.

An rika yada rade-radin cewa Mudassir Mai kusumbi ya dawo a kwanakin baya, sai dai lokacin da Aminiya ta tuntubi mahaifiyarsa Hajiya Bilki kan hakan, ta ce har yanzu ba su samu labarinsa ko wanda ya gan shi ba. “Mu dai har yanzu ba mu samu labarin inda yake ba, haka kuma ba mu taba jin wani ya ce an gan shi ba. Sai dai a matsayinmu na Musulmi har yanzu ba mu fidda ran ganinsa ba. Muna addu’ar Allah Ya bayyana shi,” inji ta.
Da take tuna irin rayuwar da danta ya taso a ciki, Hajiya Bilki ta ce ta sha wuya wajen renonsa kasancewar tunda ta haife shi yake cikin rashin lafiya. “Tunda aka haife shi nake wahala da shi, ina iya tunawa sai da na rasa duk kadarar da na mallaka wajen nema masa magani,” inji ta.
Hajiya Bilki ta nemi jama’a su taya su addu’ar Allah Ya bayyana danta wanda ta ce tun lokacin da ya bace take cikin jimamin rashinsa.
Zuwa yanzu dai Muda kamar yadda ake kiransa wanda ba a san makomarsa ba, wani yayansa ya sanya wa dansa sunansa kamar yadda mahaifiyarsa ta bayyana wa Aminiya. “Yau ba a fi mako biyu ba, matar yayan Muda ta haihu sai mahaifin yaron ya mayar da sunan Muda din. Kin ga idan Muda ya mutu ya samu magaji idan kuma Allah Ya bayyana shi Alhamdulillah,” inji ta.