Har Yanzu Ba mu Ga ‘Ya’yanmu Ba — Iyayen ‘Yan Matan Jami’ar Gusau
Kakakin rundunar ’yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar ya ce, ba su samu labarin sakin yaran ba.
Iyayen ‘yan matan da aka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya ta Gusau a Jihar Zamfara, sun ce ba su da labarin sakin ’ya’yansu a hukumance.
Kafafen sadarwa musamman na intanet sun ruwaito cewa an saki sauran ‘yan matan guda tara da suka rage a hannun ‘yan bindigar.
A watan Satumbar 2023 ne dai ‘yan bindiga suka kai hari gidajen ‘yan matan da ke daura da jami’ar a Unguwar Sabon Gidaa birnin Gusau.
Mahaifin ɗaya daga cikin ‘yan matan, Dokta Ibrahim Mai Unguwa ya bayyana wa Aminiya ta wayar tarho cewa shi dai har yanzu a kafafen sada zumunta yake ganin labarin an saki ‘ya’yan nasu, har ma an damka su ga hukumomin tsaro.
- Yadda tsadar takin zamani ke neman hana noman rani a Kano
- Wadanda suka kashe dakarunmu za su ɗanɗana kuɗarsu — Tinubu
Ya ce “Gaskiya babu wanda ya kirani daga makaranta ko hukumomin tsaro dangane da sakin yaran.
“Ni ma ta kafafen sada zumunta na ga ana cewa an saki ‘ya’yan namu, sai kuma a bakin jama’ar gari da kai da ka kirani.
Dokta mai Unguwa ya ce zai fi kowa farin ciki idan ta tabbata an saki yaran, kuma yana rokon Allah Ya tabbatar da sakin ‘ya’yan nasu.
Shi ma dai Alhaji Ibrahim Malami, mahaifin ɗaya daga cikin ‘yan matan ya bayyana mana cewa ya ji kafar Labarai ta BBC ta bayyana cewa an sako biyar cikin ‘yan matan da aka yi garkuwa da su, amma bai samu labarin daga hukumar makaranta ko hukumomin tsaron Najeriya ba.
A nasa bangaren, shugaban jami’ar, Farfesa Mua’azu Abubakar ya bayyana cewa, “ A kafafen sada zumunta na ga batun sakin yaran, amma ina da yakinin cewa hukumomin tsaro na yin duk abin da ya dace a matsayinsu, amma ba ni da labarin sakin yaran.”
Shi ma dai kakakin rundunar ‘yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar ya ce, ba su samu labarin sakin yaran ba.