Har yanzu ba mu gano musabbabin mutuwar jami’inmu ba-’Yan sandan Legas
Ga dukkan alamu har yanzu tsugune ba ta kare ba dangane da mutuwar jami’in dan sanda, SP Nwaoha Uzoma, mai kula da oifishin ’yan sandan yankin Ijede da ke Jihar Legas, domin rundunar ’yan sandan jihar ta ce har yanzu ba a tantance abin da ya kashe shi ba.Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan […]
Ga dukkan alamu har yanzu tsugune ba ta kare ba dangane da mutuwar jami’in dan sanda, SP Nwaoha Uzoma, mai kula da oifishin ’yan sandan yankin Ijede da ke Jihar Legas, domin rundunar ’yan sandan jihar ta ce har yanzu ba a tantance abin da ya kashe shi ba.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Legas, DSP Kenneth Nwosu ya bayyana cewa har yanzu ba a kai ga gano musabbabin mutuwar sa ba, amma suna ci gaba da bincike.
Ya ce ‘Ranar 25 ga watan Disamban shekarar da muke ciki da misalin karfe 8 na safe aka samu gawar Sufurtanda Nwaoha Uzoma a cikin ofishinsa da ke yankin Ijede. An dauke gawar an kai ta wurin ajiyar gawarwaki na asibitin Saint Raphael. Har yanzu ba a gano abin da ya kashe shi ba, amma ana ci gaba da bincike’.
A karshen makon da ya gabata ne aka gano gawar Sifurtanda Nwaoha Uzoma, shugaban ofishin ’yan sanda na yankin Ijade a cikin ofinsa bayan ya kulle kansa a cikin ofishin.
Binciken Aminiya ya gano cewa bayan da ya kwana daya bai bude ofishin ba, kuma bai amsa wayar da aka yi ta buga masa ba, sai aka balle kofar da karfi.
Aminiya ta gano cewa bude kofar ke da wuya sai aka ga gawarsa kwance a tsakiyar ofishin har ta fara kumbura.
Wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta ba da ke kusa da marigayi Uzoma ta bayyana cewa shi ne jami’in da yake kula da yankin Anthony kafin daga bisani a dawo da shi yankin Ijede da ke karamar hukumar Ikorodu a farkon Disambar bara.
Majiyar ta bayyana cewa marigayin dan kimanin shekaru 50 a duniya ya mutu ya bar matar aure daya da ’ya’ya.
Wata majiya da ke kusa da shi ta bayyana cewa ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a lokacin da aka dawo da shi yankin Ijede, amma daga bisani ya samu sauki sosai.
Majiyar ta ce Uzoma mutum ne mai fara’a, wanda idan aka bata masa rai kuma aka nemi yafiyarsa yake yafewa, ya mayar da komai ba komai ba.
Majiyar ta ce ya shiga ofishinsa ya kulle kansa da farko mutane ba su tsargu ba, sai daga bisani bayan da bai bude ofishin ba a washegari mutane suka fara tsarguwa. Daga bisani aka balle ofishin, inda aka ga gawarsa a tsakiyar ofishin.