Har yanzu ba mu yanke shawara kan sake tattaunawa da Amurka ba — Iran

Duk da furucin Amurka na son inganta hulɗar jakadanci da Iran, a aikace tana ɗaukar matakan da ke nuna akasin haka.

Har yanzu ba mu yanke shawara kan sake tattaunawa da Amurka ba — Iran

Lokacin da mataimakin shugaban ƙasar Amurka, JD Vance ya sauka a Pakistan a shirye-shiryen tattaunawa da Iran

Hukumomin Iran sun ce har yanzu ba su yanke hukunci kan ko za su halarci zagaye na gaba na tattaunawa da Amurka ba, wanda ake sa ran za a gudanar a Islamabad, babban birnin Pakistan.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na mako-mako, inda ya ce har yanzu babu wata tsayayyar matsaya kan batun.

“Ya zuwa yanzu, ba mu da wani shiri na shiga zagaye na gaba na tattaunawa, kuma ba a yanke hukunci a kai ba,” in ji shi.

Rahotanni sun nuna cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran da Amurka suka cimma za ta ƙare a ranar 21 ga wannan wata, abin da ke nuni da yiwuwar sake tsanantar rikici idan ba a cimma wata sabuwar matsaya ba.

Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wutar, tana mai cewa ta datse mata zirga-zirgar jiragen ruwa tare da kai hare-hare, zarge-zargen da ke ƙara dagula dangantakar ƙasashen biyu.

Haka kuma, Baqaei ya musanta iƙirarin da Amurka ta yi na cewa ba a haɗa batun tsagaita wutar Lebanon cikin tattaunawar ba, yana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne, tare da buƙatar a sanar da Pakistan — wacce ke shiga tsakani — halin da ake ciki.

Ya ƙara da cewa duk da furucin Amurka na son inganta hulɗar jakadanci da Iran, a aikace tana ɗaukar matakan da ke nuna akasin haka.

Bugu da ƙari, ya jaddada cewa Iran ba za ta amince da duk wani wa’adi daga wata ƙasa ba idan hakan ya ci karo da muradunta, yana mai cewa batun shirinta na nukiliya ba wani abu ba ne da za a tattauna a kai.

Tun farko dai tattaunawar da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu a Pakistan ta gamu da cikas, inda aka rabu ba tare da cimma matsaya ba a ranar 12 ga watan Afrilu.

A nata ɓangaren, Amurka ta ce mataimakin shugaban ƙasar, JD Vance, ne zai jagoranci tawagar ta zuwa tattaunawar, yayin da Pakistan ta nuna ƙwarin gwiwar cewa za a samu halartar ɓangarorin biyu domin nemo mafita.