Har yanzu ba mu yanke shawara kan sauya tufafin NYSC ba — Ministan Matasa

Ministan ya ce duk wata matsaya da za a cimma za ta fito ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Har yanzu ba mu yanke shawara kan sauya tufafin NYSC ba — Ministan Matasa

Ministan Matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta cimma matsaya ba kan  batun sauya tufafin masu yi wa ƙasa hidima na NYSC.

Ayodele ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X da yammacin ranar Alhamis, yana mai bayyana wasu rahotanni da suka yi wa kalamansa na bayan nan gurguwar fahimta.

Ministan ya ce ambaton yadin Adire, Atampa da Kampala da ya yi a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels misalai ne kawai ya bayar, amma har yanzu babu wata matsaya da aka cimma dangane da sauya kakin da masu yi wa ƙasa hidima ke amfani da shi a yanzu.

“Manufar ita ce na bayar da misalai na wasu daga cikin shawarwarin da aka gabatar yayin tattaunawa. Amma ban sanar da cewa an amince da wani irin kaya da zai maye gurbin kakin NYSC na yanzu ba,” in ji shi.

Ministan ya ce duk wata matsaya da za a cimma za ta fito ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da la’akari da abin da ya fi amfani ga shirin NYSC da kuma Najeriya baki ɗaya.

Ya kuma ce bai kamata muhawarar da ake yi kan kayan NYSC ta ɗauke hankalin jama’a daga manyan sauye-sauyen da gwamnati ke shiryawa domin ƙarfafa matasan Najeriya da kuma bunƙasa ci gaban ƙasar ba.