Har yanzu babu ɓullar cutar kwalara a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta musanta rahotan da hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa ta fitar.

Har yanzu babu ɓullar cutar kwalara a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin Kano ta musanta rahotan ɓullar cutar kwalara a jihar da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Wannan na zuwa ne bayan Cibiyar Yaki da Yaɗuwar Cututtuka ta Najeriya NCDC ta sanya Jihar Kano cikin jihohi 31 da ke fama da cutar.

Sai dai jami’in hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Kano, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa Aminiya a ranar Laraba cewa bayanai sun nuna cewa jihar ba ta fuskantar cutar ta amai da gudawa.

Ya ce, “A bisa binciken da muka yi ya zuwa yanzu, babu ɓullar cutar kwalara a Kano. Ba mu da rahoton ɓullar cutar ko guda har yanzu.

“Mun ga wasu rahotanni a kafafen yaɗa labarai, amma muna mai sanar da cewa babu ko mutum ɗaya da ya kamu da cutar a jihar.”

Aminiya ta samu rahoton cewa Hukumar NCDC ta ce ana zargin kimanin mutane 1,141 ne aka samu daga watan Janairu zuwa Yunin bana yayin da aka tabbatar mutum 65 sun kamu a fadin Nijeriya.

Ya zuwa ranar 12 ga watan Yuni, an bayar da rahoton mutuwar mutane 30 daga ƙananan hukumomi 96 a cikin jihohi 30, inda aka ce Kano ta samu mutum 13 da aka tabbatar da sun kamu da cutar, sai kuma mutum ɗaya da ya rasu.

A cewar hukumar, ya zuwa yanzu, adadin waɗanda suka mutu ya kai 34 yayin da aka tabbatar mutum 1,288 sun kamu da cutar.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka