Har yanzu babu coronavirus a Kogi – Yahaya Bello
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ce har yanzu babu cutar coronavirus a jiharsa kuma ya janye dokar kullen da ya kakaba tun farko a Karamar Hukumar Kabba sakamakon zargin annobar. Gwamnan ta wata sanarwa a ranar Juma’a a Lokoja, ya ce matakin ya zama wajibi saboda gwajin cutar da aka yi ya tabbatar duk […]
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ce har yanzu babu cutar coronavirus a jiharsa kuma ya janye dokar kullen da ya kakaba tun farko a Karamar Hukumar Kabba sakamakon zargin annobar.
Gwamnan ta wata sanarwa a ranar Juma’a a Lokoja, ya ce matakin ya zama wajibi saboda gwajin cutar da aka yi ya tabbatar duk wadanda aka dauki jininsu ba su dauke da ita.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai gwamnan ya sanya dokar ta tsawon kwanaki 14 yayin wani jawabi da ya gudanar ga al’ummar jihar.
Ya kuma shawarci jama’a da su rika bin shawarwarin Hukumar Kiyaye Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) don kiyaye yaduwar cutar a jihar.
Yahaya Bello ya kuma ba da umarnin raba kayan tallafi ga mazauna karamar hukumar Kabba, sannan a bi gida-gida don zakulo wadanda ake zargin sun yi mu’amala da wanda ake zargi ya fara kamuwa da ita a garin na Kabba.
A baya dai an yi ta samun sabani tsakanin gwamnatin jihar ta Kogi da ta Tarayya kan batun annobar. Jihar ta yi zargin ana so a kakaba mata cutar ne duk kuwa da cewa ta dage cewa babu ita a jihar.