Har yanzu ban san mahaifina ba – ’Yar fim Shan George

Shan George, ’yar fim din da ta yi fice a fina-finan Kudancin Najeriya ta koka tare da nuna alhininta na rashin sanin inda mahaifinta yake. Ta fada wa mujallar ‘Showtime’ cewa har yanzu ba ta san mahaifin nata a zahiri ba.“Da ma a ce na san mahaifina, da na ji dadi.” Inji ’yar fim din. […]

Har yanzu ban san mahaifina ba – ’Yar fim Shan George

’Yar fim Shan GeorgeShan George, ’yar fim din da ta yi fice a fina-finan Kudancin Najeriya ta koka tare da nuna alhininta na rashin sanin inda mahaifinta yake. Ta fada wa mujallar ‘Showtime’ cewa har yanzu ba ta san mahaifin nata a zahiri ba.
“Da ma a ce na san mahaifina, da na ji dadi.” Inji ’yar fim din. “Ni kadai ce mahaifiyata ta haifa kuma babana Bature ne. Mahaifiyata mace ce mai nagarta, mai halayen kwarai amma har yanzu ina takaici da alhinin rashin sanin mahaifina. A kullum ina cikin tunanin ko yaya mahaifina yake? Na yi kokari da hakilon gano inda yake amma haka ta ta gaza cimma ruwa.”
’Yar fim din, wacce ’yar asalin Jihar Kurosriba ce, wacce kuma a bana ta cika shekara 43 da haihuwa ta kara bayanin cewa: “A kokarin da nake na neman mahaifin nawa, na yi tattaki har zuwa birnin Manchester da ke Ingila amma koda na je, ban yi nasarar gano shi ba. A lokacin nan ina ’yar shekara 35 a duniya kuma tun daga lokacin na yanke tsammanin ganawa da shi.