Har Yanzu Bobrisky Na Da Mazakuta —Hukumar Gidan Yari

Hukumar gidan yarin da aka tura Bobrisky ta tabbatar da cewa har yanzu Bobrisky yana da mazakuta kamar kowane namiji

Har Yanzu Bobrisky Na Da Mazakuta —Hukumar Gidan Yari

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wata kotu dake zamanta a Legas to tura shahararren dan daudun nan Bobrisky zuwa gidan yari. 

Tun tafiyarsa mutane da dama ke tambayar a wane daki aka saka shi a gidan yarin, na maza ko na mata?

A baya dai Bobrisky ya rika bayyana cewa ya yi aiki an cire masa mazakutarsa, don haka ya zama mace.

Sai dai tun a kotu gabannin tura shi gidan yari, dan daudun ya tabbatar wa alƙali cewa shi fa namji ne.

Jaridar Punch ta tattauna da wani ma’aikacin gidan yarin da aka kai Bobrisky, sai dai ya bukaci a sakaya sunansa.

Ya ce an yi wa Bobrisky tambayoyi kamar yadda ake yi wa duk wanda aka kawo gidan yarin, an kuma saka shi a cikin ’yan uwansa maza.

“Bayan gudanar da bincike, an  tura wani ɗaki, kuma ba shi kadai ba ne a dakin. Akwai wasu fursunoni tare da shi.

“Wurin kwanciya kadai aka raba masu. Kamar gidan kwanan dalibai ne da malamin da dakin ke hannunsa zai bai wa kowane sabon dalibi daki.”

Majiyar ta kara da cewa Bobrisky yana kiyaye ka’idoji da dokokin da aka saka a cikin gidan.

“Idan lokacin darasi ya yi, yana zuwa. Idan lokacin cin abinci ya yi, zai je ya karbi nasa. Yana kiyaye duk waɗannan ba tare da nuna fifiko ko taurin kai ba.

“Tun da aka shigo da shi nan yake gudanar da harkokinsa kamar sauran fursunoni.”

Yayin da yake yin karin haske kan ikirarin cewa ana ba wa Bobrisky kariya daga cin zarafi, jami’in ya ce, gidan ya haramta duk wani nau’i na cin zarafin fursuna.

“Ba a ba shi wata kariya ta musamman. Yana bin ka’idoji kamar kowane fursuna da ke gidan yarin.

“An haramta yin luwadi kuma babban laifi ne. Luwadi ko wani abu da ya yi kama da shi duk haramun ne a wannan gidan.

“Don haka duk fursunan da ya yi yunkurin karya dokar zai fuskanci hukunci mai tsanani, ba iya Bobrisky ake karewa daga wannan ba.”

Da manema labarai suka tuntubi mai magana da yawun hukumar gidajen yarin na jihar Legas, Rotimi Oladokun, ya ki cewa komai kan lamarin.

Kawai cewa ya yi, “Ba ni da wani abin cewa.”

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos