Har yanzu City na fatan lashe Firimiyar Ingila — Guardiola

Yanzu haka dai City na matsayi na biyu a teburin gasar da maki biyar tsakaninta da ta ɗaya, Arsenal.

Har yanzu City na fatan lashe Firimiyar Ingila — Guardiola

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ce har yanzu ƙungiyarsa na fatan lashe Gasar Firimiya ta Ingila, duk da koma bayan da take fuskanta a ƙarshen kakar wasa.

Manchester City na buƙatar doke Crystal Palace a wasan da za ta buga ranar Laraba domin ci gaba da raya fatanta na kare kambun gasar.

Yanzu haka dai City na matsayi na biyu a teburin gasar da maki biyar tsakaninta da ta ɗaya, Arsenal, duk da cewa tana da wasa guda a hannu yayin da saura wasanni uku a kammala kakar.

Idan City ta kasa samun nasara a filin wasa na Etihad, Arsenal na iya lashe kofin Firimiya karo na farko cikin shekara 22 idan ta doke Burnley ranar Litinin.

Da yake magana a taron manema labarai dangane da wasan, Guardiola ya ce ƙungiyarsa ba ta fuskantar wani matsin lamba duk da kunnen doki 3-3 da suka yi da Everton a makon jiya.

“Matsin lambar dai iri ɗaya ne kamar yadda yake kwanaki biyu ko uku da suka gabata,” in ji Guardiola.

Kocin na Manchester City, wanda ke neman lashe kofin Firimiya karo na bakwai cikin kaka tara, ya ce bai tattauna da ’yan wasansa ba tun bayan wasan Arsenal da West Ham na ranar Lahadi.

Arsenal ta yi nasarar cin West Ham 1-0 bayan da na’urar taimakon alƙalancin wasa VAR ta soke ƙwallon da West Ham ta farke a ƙarshen wasan.

Guardiola ya ce a tsawon rayuwarsa ta horarwa ya fahimci duk abin da mutum ba shi da ikon juya al’amuransa ba bai kamata ya damu da shi ba.

“Abin da ya rage mana shi ne mu mayar da hankali wajen gyara kura-kuran da muka yi a bana domin ci gaba da fafatawa a gasar. Har yanzu muna cikin wannan fafatawa, kuma wasa na gaba shi ne Crystal Palace,” in ji shi.

Ya kuma ce bai damu da yiwuwar Crystal Palace ta hutar da wasu ’yan wasanta ba, duk da cewa za ta kara da Arsenal a wasan ƙarshe na kakar kafin buga wasan ƙarshe na Conference League da Rayo Vallecano.

“Kowace ƙungiya ƙwararriya ce. Crystal Palace za ta yi wasa mai zafi. Mun ga yadda Leeds ta fafata da Tottenham duk da cewa ba ta cikin masu fuskantar barazanar faɗawa rukunin Championship,” in ji Guardiola.

Kocin ya kuma bayyana cewa Rodri da Abdukodir Khusanov na samun sauƙi daga raunukan da suka ji, kuma za a yanke shawara haskawarsu a wasan bayan atisayen ranar Talata.

Manchester City za ta kara da Chelsea a wasan ƙarshe na Kofin FA ranar Asabar, yayin da take fatan lashe kofuna uku bayan ta riga ta lashe League Cup a bana.