Har yanzu dai a kan rashin tsaro a Jihar Zamfara
Annobar rashin tsaro a Jihar Zamfara siyasa ta sa an mayar da hankali ne a kan cece-kuce da zargi da mayar da martani a tsakanin juna da ya kunno kai a tsakanin Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara da Rundunar Sojin Sama kan harin da jiragen yakin rundunar suka kai kauyen Dumburum a Karamar Hukumar Zurmi da […]
Annobar rashin tsaro a Jihar Zamfara siyasa ta sa an mayar da hankali ne a kan cece-kuce da zargi da mayar da martani a tsakanin juna da ya kunno kai a tsakanin Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara da Rundunar Sojin Sama kan harin da jiragen yakin rundunar suka kai kauyen Dumburum a Karamar Hukumar Zurmi da ke jihar a ranar 9 ga Afrilu. A cece-kucen, Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara ta yi zargin cewa a harin na Dumburum, idan mai karatu na bibiyar wannan shafi makalar makon da ya gabata, an yi zargin cewa sojin sama sun kashe mutum 11, tare da jikkata wadansu, wadanda Majalisar Sarakunan ta ce dukkansu fararen hula ne da ba su ji, ba su gani ba. Ma’ana ba ’yan ta’adda ba ne da suka addabi jihar ta Zamfara da makwabtanta irin su Katsina da Kaduna.
A nata martanin, Rundunar Mayakan Saman ta dage a kan cewa a iyakacin saninta bisa ga bayanan sirrin da ta yi amfani da su kafin kai harin, mafakar ’yan ta’addan ta kai harin, don haka sai ta kalubalanci Majalisar Sarakunan ta bayyana sunayen fararen hular da ta ce an kashe din. wanda ba tare da wata-wata ba Majalisar Sarakunan ta hannun Sakatarenta kuma Sarkin Bungudu, ta kira wani taron manema labarai a Gusau babban birnin jihar ta Zamfara inda ta warware zare da abawa a kan jerin sunayen mutum 11, da ta ce harin rundunar mayakan saman ya hallaka da ma na wadanda suka jikkata.
Bayan wannan cece-kuce da ya barke tsakanin Rundunan Mayakan Saman da Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, akwai kuma sanarwar da Ministan Tsaro Birgediya Janar Mansur Dan-Ali ya bayar ta hannun kakakinsa Kanar Tukur Gusau a Abuja a daidai lokacin da Sufeto Janar na ’Yan sandan kasar nan Alhaji Muhammadu Adamu ya kai ziyara a jihar ta Zamfara ya kuma gana da dukkan masu ruwa-da-tsaki na jihar a kan batun rashin tsaro a jihar. A waccan sanarwa Minista Dan-Ali ya zargi wasu sarakunan jihar da laifin hada baki da ’yan ta’addar jihar. Zargin da shi ma ko kusa bai yi wa sarakunan dadi ba, har Majalisar Sarakunan ta kalubalanci Ministan da ya fallasa sunayen sarakunan da suke hada baki da ’yan ta’addar. Daga bisani dai Minista Dan-Ali, wanda dan asalin jihar ta Zamfara ne kuma ma mai jiran gado a Masarautar Birnin Magaji, ya fadi cewa ko kusa ba ya fadi haka ba ne don ya muzanta sarakunan, illa dai don kada su rika sare guiwar dakarun da suke yaki da ’yan ta’addar.
Kazalika sai ga shi a cikin makon jiya, Babban Hafsan Mayakan Sama Iya Mashal Sadik Abubakar ya amsa kalubalen sarakunan Zamfarar, inda ya kafa wani kwamitin bincike mai wakilai 7 a karkashin jagorancin Iya Bayis Mashal Idi Lubo, da ya dora wa alhakin lallai ya ziyarci jihar ta Zamfara tare da ganawa da dukkan masu ruwa-da-tsaki na jihar da ’yan uwan wadanda ake zargin an kashe ko an jikkata da niyyar tantance gaskiya ko rashin gaskiyar zargin.
A fara aikin kwamitin binciken ne, lokacin da ya kai ziyara a fadar Mai martaba Sarkin Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara a ranar Asabar da ta gabata, kwatsam sai aka ji Sarkin a madadin sarakunan jihar, yana neman afuwar Rundunar Mayakan Saman a kan wancan zargi da suka yi mata na kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba, mutanen da har suka iya bayyana sunayensu dalla-dalla. Kuma kwana biyu da bayyanar wancan labari, sai ga Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar ya kira wani taron manema labarai a Gusau yana musanta wancan matsayi na suna neman afuwar Rundunar Mayakan Saman.
Sarkin na Anka ya fadi cewa a duk tsawon jawabin da ya yi ba inda ya ambaci janye matsayinsu bare ya nemi afuwa. Yana mai cewa basarake irinsa bai kamata ya furta zancen da ba ya iya karewa ba, kuma taron majalisarsu ya dogara ne kacokan a kan cikakkun sahihan bayanan da suka tabbatar da cewa farar hular da ba su ji ba su gani ba ne aka kashe. Ya kara da cewa idan har basarake mai matsayi irin nasa zai yi magana sannan daga baya ya zo ya canja, wato ke nan bai cancanci rike wannan mukami ba.
Shi ma Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdu’aziz Yari a Asabar din makon jiyan an ruwaito a gidansa na garinsu Talata Mafara, lokacin da yake karbar bakuncin ayarin kwamitin binciken na Rundunar Mayakan Saman yana cewa ko kusa ba ya da wani kaico a kan harin da sojojin saman suka kai a kauyen na Dumburum da ke Karamar Hukumar Zurmi a ranar 9 ga Afrilu, inda aka kashe wadancan mutum 11 da ma wadanda aka jikkata da Majalisar Sarakunan ta dage cewa fararen hula ne da ba su ji ba su gani ba.
Gwamnan ya tabbatar wa ayarin kwamitin binciken cewa a zamansa na Gwamnan Jihar kuma Babban Jami’i mai kula da tsaron jihar kwata-kwata, babu wani lokaci da ya taba karbar rahoton da ke cewa ba ’yan ta’adda aka kashe ba farar hula ne da ba su san hawa bare sauka. Don haka sai ya bayyana rashin jin dadinsa a kan yadda Sarkin Zurmi wanda da kansa wata rana ya taba rokonsa a kan yadda gwamnati za ta tarwatsa kauyen na Dumburum, kasancewarsa ya zama sansanin ’yan ta’adda, amma kuma inji Gwamna Yari abin mamaki sai ga shi, Sarkin na Zurmi, ya koma ya hada kansa da ’yan uwansa sarakunan jihar sun dage wajen ba da shelar fararen hula aka kashe, ba ’yan ta’adda ba.
Mai karatu, daga wannan dambarwa da aka shiga tsakanin manya-manyan masu ruwa-da-tsaki a Jihar Zamfara a kan annobar ta’addancin masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kai hare-hare da kona gidaje da kadarorin mutanen jihar, na dade ina ta tunanin me ya kai sarakunan jihar shiga cikin wannan dambarwa. Shin jihar ta Zamfara ba ta da kwamitin dattawa kamar yadda ake da su a jihohi irin su Katsina da Borno da sauransu ne? Ga ni na yi tunda aka fara rikicin Kungiyar Boko Haram a Jihar Borno yau kusan shekara goma, zai yi wuya ka ce ga lokacin da ka ji sarakunan jihar sun tsoma kansu ciki. sai dai a kullum ka ji kiraye-kirayen kungiyar dattawan jihar ta Borno, duk kuwa da bambancin addini da ake da shi a tsakanin mutanen jihar.
Da wannan hali da aka shiga a jihar ta Zamfara, mai karatu, ka iya hasashen cewa kwamitin binciken, ba wani rahoto na daban zai fitar ba, da ya wuce wanda kake ji yanzu, bare ya ce ga mai laifi, ga kuma irin hukuncin da za a yi masa, ko musu, bisa ga bambancin matsayi da aka samu tsakanin gwamnatin jihar da sarakunan jihar. Da wannan ka iya cewa batun ya zama siyasa. saura da me? Kamanta gaskiya da adalci, musamman daga mahukunta da rungumar kowa da kowa, ta yadda kowa zai ji ana yi da shi da komawa ga Allah (SWT) bil hakki da gaskiya, su kadai za su fitar da mu daga wannan mawuyacin hali da muka samu kanmu ciki, na rigingimu da fadace-fadace, masu kama da na addini da kabilanci da sauran miyagun ayyuka da suka game kasa.