Har yanzu Fulanin da alkali ya yi wa gwanjon shanunsu na jiran tsammani

Al’ummar Fulanin garin Katuna da ke yankin Kodo a karamar Hukumar Bosso a Jihar Neja na jiran tsammani bayan shafe fiye da shekara suna jira gwamnati ta tallafa musu bayan da tsohon Alkalin Kotun Zungeru Malam Aminu Kagara ya jefa sa aka yi gwanjon shanunsu 259 da tumaki da awaki 187 a kasa da Naira […]

Har yanzu Fulanin da alkali ya yi wa gwanjon shanunsu na jiran tsammani
Har yanzu Fulanin da alkali ya yi wa gwanjon shanunsu na jiran tsammani

Al’ummar Fulanin garin Katuna da ke yankin Kodo a karamar Hukumar Bosso a Jihar Neja na jiran tsammani bayan shafe fiye da shekara suna jira gwamnati ta tallafa musu bayan da tsohon Alkalin Kotun Zungeru Malam Aminu Kagara ya jefa sa aka yi gwanjon shanunsu 259 da tumaki da awaki 187 a kasa da Naira miliyan 10 da sunan biyan diyyar wani matashi da aka sare wa hannu lokacin da suka yi rikicin a tsakaninsu.

Wakilinmu ya sake zuwa garin na Kotuna domin sauraron yadda suka yi ta gudanar da rayuwarsu daga ranar 25 ga watan 3 na shekarar 2014 da aka sauya musu daga na kiwo zuwa wasu daban-daban.
Malam Haruna Suleiman Utono shi ne jagoran Fulanin ya shaida wa wakilinmu cewa tuni suka kai tsohon alkalin kara domin a bi musu kadin al’amarin da ya jefa mutanensa a ciki fiye da shekara daya da ta wuce. Ya ce, “Ka san yadda lamarin kotu yake yau ne a zauna, gobe a dage. Babban abin da muke tsoro shi ne, wadannan mutanen da aka raba da dabbobinsu, suna dogaro ne da su domin gudanar da rayuwarsu. Lokacin da al’amarin ya faru,sun yi niyyar daukar matakin da inda an bari ba zai yi kyau ba ko kadan. Dattawa da manyan gari da mu da muke jagorancin maganar ne muka yi ta ba su baki a kan su yi hakuri. Don haka, shirun da suka ji ya sa suke kokarin sake tunani game da lamarin.”
Jagoran ya nemi gwamnati ta dauki matakan da suka kamata domin taimaka wa mutanen, ya ce, “Mutanen sun yi fice wurin noma da kiwo a tsawon lokacin da suka shafe a yankin, ba tare da dogaro da takin zamani ba, saboda dabbobinsu suna samar musu da takin da suke noma duk shekara.”
dan Agwai Shehu mai kimanin shekara 14 maraya ne kuma yana daya daga cikin wadanda aka yi awon gaba da shanunsa da ya gada daga wurin mahaifinsa, ya shaida wa wakilinmu cewa, “A gaskiya rayuwa ta yi mini kunci don na rasa duk abin da na mallaka, tufafin da kuka ga na sa a jikina wani bawan Allah ne ya ba ni domin in samu abin da zan rufe tsiraicina.”
Ya ci gaba da cewa, “Sana’ar da na fara yanzu ita ce sassaben itacen doya da nake sayarwa. Idan Allah Ya ba ni sa’a na samu guda 150 shi ne ake saye kan Naira 100. Da kyar mutum ya hada Naira 300 a yini ka ga kuwa wannan sana’ar tana da matukar wahala, sannan ba a samun itatuwan kamar da, don muna da yawa wadanda muke neman na rufin asiri.”
Shi kuwa Malam Ori Abubakar wanda yake da marayu hudu a gabansa bayan da matarsa ta rasu kafin aukuwar lamarin ya ce, ’yan uwa da abokan arziki ne suke tallafa masa daga lokacin da suka fada cikin wannan mummunan hali domin samun abin rufin asiri. Ya ce duk da yana samun irin wannan talafin, bai dogara kacokan a kansa ba, yana hadawa da aikin kwadago.
Malam Ori ya nuna takaicinsa kan yadda gwamnati ta yi musu alkawarin tallafa musu don rage radadin asarar da alkalin ya jawo musu. Ya ce yana da shanu 27 da tumaki 21 mallakinsa da alkali ya kwace da sunan diyya.
Ya ce “Wallahi rashin cika alkawarin da gwamnatin Mu’azu Babangida Aliyu ta yi ya sa mun yanke kauna daga gwamnati, sai dai muna sa ran mutanen da muka zaba da suka hada da dan majalisarmu ta jiha Malam Maliki Madaki da na Wakilai, Malam Salihu Adamu Shadafi da kuma Gwamna Abubakar Sani Bello da Sanata Dabid Umaru da Shugaban kasa Muhammadu Buhari za su taimaka mana.”
Barista Muhammad El-Surur Abubakar shi ne lauyan mutanen ya shaida wa wakilinmu cewa daya daga cikin dalilan da suka sa shari’ar da suka shigar ke tafiyar hawainiya, ba ya rasa nasaba da yadda yanayin tafiyar da shari’a yake a kasar nan na a zauna yau a dage gobe. Ya ce, “Duk da haka muna sa ran samun adalci daga wurin alkalin wanda kowa ya san mutum ne da ya kware a aikinsa kuma ba a san shi da zalunci ba.”
Barista El-Surur wanda ya tabbatar da mawuyacin halin da Fulanin suka shiga ta amfani da karfin doka da tsohon alkalin ya yi, ya ci gaba da cewa, “A wasu lokutan ni ke shiga gaba domin agaza musu da kayan abinci don raba su da yunwa, wannan zaluncin har ina?”
Lauyan ya tabbatar cewa za su ci gaba da ba mutanen baki domin hana su aikata duk wani abin da ya saba wa doka, inda ya ce har yanzu wannan al’amarin yana kamar danye ne a wurinsu shi ya sa kafarsa ba ta yankewa a tsakaninsu.
Ya ce za su nemi hanyar fahimta da sabuwar gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello domin share wa Fulanin hawayensu.