Har yanzu ina cikin aikin soja, Inji Manjo Almustafa
Wakilin Aminiya ya tattaunawa da Manjo Hamza Almustafa kan batutuwa da dama tun bayan fitowarsa daga gidan yari, kamar haka:AMINIYA: Ka yi watanni da fitowa daga gidan yari, amma jama’a na ta shaci-fadi kan kana soja ko ka bari, yaya lamarin yake ne?ALMUSTAFA: Kamar yadda na yi bayani, yau wata na 5 da ’yan kwanaki […]
Wakilin Aminiya ya tattaunawa da Manjo Hamza Almustafa kan batutuwa da dama tun bayan fitowarsa daga gidan yari, kamar haka:
AMINIYA: Ka yi watanni da fitowa daga gidan yari, amma jama’a na ta shaci-fadi kan kana soja ko ka bari, yaya lamarin yake ne?
ALMUSTAFA: Kamar yadda na yi bayani, yau wata na 5 da ’yan kwanaki da fitowa, alhamdulillahi, abubuwan da ka ga ina yi, abubuwan da na fada ne tun 1984, na taimaka wa matasa wajen nema musu ayyuka da makarantu da dai abin yi, domin maganin zaman-banza, kuma ya kamata a taimaka musu. Batu na gaskiya shi ne Arewa tana neman taimako kuma mun dade muna bauta mata, kuma mu ’ya’yanta ne, don haka za mu ci gaba da yi mata hidima har abada. A nan muke. A nan muka tsaya, kuma za mu ci gaba da kyautata mata. Nauyi ne da ke kan duk wani wanda zai so a ce shi da ne nagari, kuma taimakon, ba sai jiharmu ba ko garinmu. Wannan ne na sa gaba, shi kuma nake yi a halin yanzu.
AMINIYA: Ina batun aikin soja?
ALMUSTAFA: Wato a aikin soja, idan aka kai ka kara kotu, to akwai matakai da ake dauka. Gwamnatin Jihar Legas ta daukaka kara, sai an kammala wannan abu ne daki-daki, kana hukumar soja, a bisa dokar kasa da dokar soja, ita kuma ta duba batun gaba daya, kana ta yanke nata hukuncin. To ganin maimakon in zauna haka nan shi ya sa nake wadannan abubuwan da nake yi, wanda ka ce a ji ni nan yau, gobe a ji ni ina can.
AMINIYA: Ana rade-radin wai fitowarka da hannun gwamnatin tarayya a ciki, kuma ta fidda kai ne domin tana son ta yi amfani da kai saboda cimma manufarta ta siyasa, me za ka ce?
ALMUSTAFA: Na ji, kuma masu wannan batu ba su da hujja. Kotu ta sake ni ne bisa ga hujjar cin amanar da aka yi mana. Kai Ladan kana nan gabanka mai shari’a a kotun daukaka kara ta share sama da minti goma tana karanta abubuwan da ta yi rantsuwa da su da baibul da ta yarda da shi cewa za ta yi hukuncin gaskiya kuma a kan tsoronta da Allah kan wannan batu. Shi ne ta karanta hukuncin gaban duniya, ta kawo hujjojinta da ya sa ta sake ni. Wadanda suka azabtar da ni ba su taba tsammanin za a cire ni ba, su sun sha yi mini alkawarin mutuwa, ido-da-ido, sun sha yi mini alkawarin ba zan yi wata daya a raye ba. a dake ni, a kona ni da wuta, a rataye ni. Yanzu ba daga asibiti nake ba? Ai naje asibiti kan raunukan da suka yi min. Daga ni har iyali har iyaye har ’yan uwa, ba wanda bai azabta ba, daga hannun wadannan mutnen, ni na ce na yafe, idan kuma yafewar ce ke damun su a kan cewa ba su sani ba, suke ci gaba da makirce-makirce, to wannan wani abu ne kuma daban. Ni dai na san ina da akida, kuma na san irin tarbiyyar da aka yi mini. Kishi da tarbiyya da rikon gaskiya da kare kasa ta ’yan uwa, shi ne abin da muka sa a gaba.
AMINIYA: Game da kalubalantar tsohon shugaba Obasanjo, ganin ka taba fadin cewa gwamnatin tarayya ta kwashe maka wasu bayanan sirri, ya za ka yi abin a kaddara ya karba bukatarka, duk da yake bai ambata sunanka ba a wasikarsa?
ALMUSTAFA: Ba na shakka, idan a yanzu Obasanjo ya karba, wallahil azim, zan yi sujudar gode wa Ubangiji, don na san zaman zai haifar da wani abu na ilmantar da Najeriya. Zai samar da wani haske, wanda zai taimaka wa na kasa, kuma zai taimaki Najeriyan kwarai da gaske. Maganar kwashe kayana, wannan gaskiya ne, lokacin da aka kama ni, duk abubuwan da nake da su, an kwashe, ba ni da komai banda kayan da ke jikina, amma maganar wasu hujjoji, a ko’ina suke a duniya, wannan wani abu ne wanda yake sirrina ne. Kai ka bari ka gani, ka taya ni addu’a Allah Ya sa ya amince cewa ni da shi za mu zauna mu yi magana a kan abubuwan da suka addabi wannan kasar. Nan za ka fahimci me nake nufi. Game da kiran suna, ai da ya kira sunana da ka ji irin martanin da zan bayar, amma tunda bai kira sunana ba, shi ya sa nake kalubalantarsa. Ba cika baki ba, ni ba irin mutanen nan ba ne masu fankama, ko girman kai, a’a, idan gaskiya ta tashi fitowa dole karya ta kauce, kuma za mu yi shi ne cikin ladabi da biyayya.
AMINIYA: Daga abin da na fahimta da kai, ka san harkokin tsaron kasar nan, yanzu idan gwamnatin tarayya ta bukace ka kan wannan bangare za ka amsa?
ALMUSTAFA: Abin da ka ga zai cutar da Najeriya da abin da kuma za ka yi wajen taimaka wa al’umma, cikin tsoron Allah, cikin gaskiya, to dukkan da nagari, bai kamata ya guje shi ba. To in sun kira ni, dayake kowane abu yana da tashi hujjar (sharadi), zan ba da hujjojina (sharuddana) na yin aikin, idan sun amince, sai na yi idan kuma ba su amince ba, sai a daina. Ni ba na yin abu kan munafunci ko kuma take gaskiya ko kuma wulakanta mutane, ko kuma cutar da mutane, bai yiwu ba a da, kuma ba zai yiwu ba a yanzu.
AMINIYA: Yaya batun kiraye-kirayen jama’a na ka shiga siyasa, mene ne ra’ayinka?
ALMUSTAFA: kwarai da gaske suna ci gaba da wannan kiran. Na tafi Kaduna da Jos wajen da aka yi fadace-fadace, domin taimakonsu da gyaran masallatansu da makarantunsu da wajen ba su abinci da magani, mutane da yawa a wadannan wuraren suna ta wadannan kiraye-kirayen, amma ni wannan bai shiga hankali na ba tukunna. Arewar da sani kafin a daure ni da Arewar da nake gani yanzu ta canza, abin da nake fata shi ne Allah Ya kawo wa kasar nan dauki da taimako ga talaka. Duk wadannan shugabannin matasan da kake gani nan sun zo ne daga sassan kasar nan daban-daban, a kan yadda za mu taimaki matasa, kuma muna nan muna yi. Yanzu haka mun hada hannu da wani mai gonar kaji, dan kasar Kenya, matasa dubu 10 ne za a samar wa aikin yi na kiwon kaji, a sassan kasar nan daban-daban.