Har yanzu Jam’iyyar PDP tana cikin zukatan Sakkwatawa –Abdullahi MD
Alhaji Abdullahi Muhammad, wanda aka fi sani da MD, jigo ne a Jam’iyya PDP, sanannen dan kasuwa a Jihar Sakkwato, ya bayyana wa Aminiya, a tattaunarta da shi, irin rikita-rikitar ’yan takarar Gwamna da jam’iyyarsu ke fama da ita da kuma dangantakarsu da tsohon Gwamna Bafarawa da dalilinsa na daukar bangaren dan takara daya da […]
Alhaji Abdullahi Muhammad, wanda aka fi sani da MD, jigo ne a Jam’iyya PDP, sanannen dan kasuwa a Jihar Sakkwato, ya bayyana wa Aminiya, a tattaunarta da shi, irin rikita-rikitar ’yan takarar Gwamna da jam’iyyarsu ke fama da ita da kuma dangantakarsu da tsohon Gwamna Bafarawa da dalilinsa na daukar bangaren dan takara daya da sauran batutuwan da suka shafi jam’iyyar:
Aminiya: A matsayinka na jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato me ya sa ka dauki bangaren Yusuf Suleiman daga cikin mutum uku da ke neman kujerar Gwamna?
Abdullahi MD: A nan Jihar Sakkwato, kowa ya san wane ne ni ga akidar siyasa, na dauki Yusuf saman kowa ne a ’yan takarar da muke da su saboda Yusuf ba ya da wata akida sai ta tausayin talaka domin in don kudi ne ba zai zo neman wannan kujera ba, yana kallon halin da Sakkwatawa suka shiga ne ya zo a nema wa jama’ar jihar nan mafita. Tuntuni duk inda Yusuf yake za ka ga talakawan jihar nan na tare da shi. Gidansa ba ya da shamaki duk wanda ya je masa da matsala zai yi kokarin magance masa, ba je ka, ka dawo. Tsohon Minista ne mai kishin jihar nan ban san wani mai kishin jiharmu fiye da shi ba, kan haka yake son canja ragamar jihar don kawo canji mai amfani da alfanu. Wadannan na daga cikin manyan dalilan da suka sanya ni na bi tafiyar Yusuf Suleiman a cikin wannan jam’iyya tamu ta PDP.
Aminiya: Amma a halin yanzu jam’iyyar tana da ’yan takarar Gwamna hudu ba wanda ya kwatanta aiki kamar Yusuf da kake goya wa baya?
Abdullahi MD: Tirkashi, Mataimakin Gwamna Mukhtari Shagari ya yi Minista shekara shida da wata bakwai a rigar PDP, yana Mataimakin Gwamna shekara bakwai yanzu, amma me ya dawo yi wa jama’ar Sakkwato? Shi kuwa Ambasada Wali ya yi Sanata kuma a yanzu yana Ambasada kusan shekara 13, duk wani yaro dan shekara 13 a jihar nan bai san da Wali ba, domin tunda aka kayar da shi a shekarar 2003 bai sake dawowa ba, sai yanzu. Sanata Gada ya yi Sanata ya kuma shugabanci wasu kwamitoci a Jam’iyyar PDP, kuma ba wani amfani da ya kawo Sakkwato, to su kadai aka yi wa PDP da ba su bari wasu su amfana ko su kawo gyara. A cikinsu ba wanda ya sadaukar da kansa kamar Yusuf Suleiman wanda ya ajiye kujerar Minista don ceton talakawa.
Aminiya: A matsayinka na dan kasuwa kuma dan siyasa ba ka ganin wasu na iya tunanin ka bi Yusuf Suleiman ne saboda idan ya samu nasara ya kara habaka kasuwancinka?
Abdullahi MD: Ban goya masa baya ba saboda ni kaina ba, ban bi shi ba don kaina kadai ba, na bi shi ne domin na san zai iya, yana da zurfin tunanin da zai kawo wa Sakkwato ci gaba, na san shi sosai dukiyar gwamnati ba za ta tsone masa ido ba. Idan ya zo Sakkwato yana ganin yadda jama’a ke tururuwa gidansa don neman taimako, kuma wannan gwamnati mai ci ta kasa magance talauci a jihar, ganin haka ya sa ya ce bari ya zo a samar da sauyin da kowane magidanci a jihar zai fi karfin abin da zai ci ba tare da ya je gidan wani maula ba.
Hakika ni dan kasuwa ne mai son canji, kuma na bi wannan tafiyar ce don in taimaka da dan tunanina a kawo wa jihar nan canji mai ma’ana. Talaucin da ke addabar jihar nan ba wai ba kudi ba ne, a’a mutum daya ne ya rike kudin daga shi sai wanda yake so. Kowane wata akan aiko mana da kudi daga Asusun Tarayya, amma sai su yi batan dabo, ya mayar da su nasa, ko kwangila ba wani dan Sakkwato da ke kwangilar Naira miliyan 100 a wannan gwamnati me zai hana talauci ya mamaye mu? Matasanmu na kara zama a gari banza an kira wasu daga Kano Legas da sauransu an mika musu saboda wata alaka. In ka tambaye su dalilin yin haka sai su ce wai ‘dan Sakkwato in ya yi karfi bai biyayya.’ In ka tafi kasuwa ’yan kasuwa barci suke yi kawai, ba wani bangare da gwamnatin nan ta taimaka. Saboda haka muka ga in har ba mu sa hannu aka kawo canji ba, to lallai za mu iya kasa kwana a gidajenmu. Ba wata gwamnati da ke kiyayya da talakawanta fiye da gwamnatin Wamakko, ina kalubalantarsu su fadi wani abu da suka yi wa wannan jihar da har wani matashi namiji ko mace ke iya barci ya yi marmarin Allah Ya tada shi gobe a samu irin wannan gwamnati. Me ta yi maka yau ko jiya balle ka yi marmarinta gobe?
Aminiya: Talakawan Jihar Sakkwato na ganin da ’yan adawa da masu rike da gwamnati kusan duk daya ne, kowa dama yake son samu amma ba a nufin talaka ba, me Yusuf ya yi wa jihar nan da kake ganin ya bambanta da saura da zai kawo wa jama’a ci gaba?
Abdullahi MD: Alal misali lokacin da ya yi Ministan Sufuri, ya yi kokarin kawo hanyar jirgin kasa daga Abuja zuwa Sakkwato wadda ake yi yanzu, da ba a canja masa wuri ba na tabbata da yanzu an kammala ta.Kuma ya raba wa kananan ’yan kasuwa jari, ga daukar nauyin karo karatu ga dalibai, a kwanan nan ma ya biya wa dalibai 300 kudin makaranta a Jami’ar danfodiyo wanda gwamnati ta gagara biya. Ya dauki samari da dama aiki kuma ya yi tsaye duk wata dama da ’yan Sakkwato suka samu bai bari ta kubce musu ba. Ba a Sakkwato kadai ba duk Arewa sai ka samu aikin da Yusuf ya yi kokarin aiwatarwa a lokacin yana Minista.
Aminiya: Ba ka ganin kun makara a yanzu da Sakkwatawa suka dawo daga rakiyar PDP?
Abdullahi MD: Wa ya fada maka haka, ba gaskiya ba ne kuma yanzu kai ya waye kusan duk a nan jihar mu Musulmi ne ba wanda zai yaudare mu da addini, domin duk inda ya gyaru in gidanka yana lalace to akwai matsala. Don haka yanzu mutum ake yi ba wai jam’iyya ba, in jam’iyya ta tsayar da mai kyau a zabe shi, don haka harkar Sakkwato ba zancen addini domin dukanmu Musulmi ne kuma PDP din Sakkwato ake magana, kada wani ya zo mana da wata rikita-rikita. Allah Yake ba da mulki ga wanda Ya so, martabar Sakkwato muke son ta dawo, kambin talaucin da muka samu har sau biyu muke son kawo gyara a ba wasu kuma.
Aminiya: Kwanan nan jami’an tsaro sun cire allunan ’yan takarar APC da PDP a wasu sassan jihar me za ka ce kan wannan lamarin?
Abdullahi MD: A wannan jiha tamu ba a taba fuskantar cire-ciren allunan ’yan takara ba, sai a wannan lokacin da Gwamna Wamakko ya rasa magoya baya, ya hada kai da hukumar tsaro don a cire mana namu a wasu wurarare shi ko aka bar nasa don kawai yana Gwamna, ka je gidan gwamnati ka gani za ka samu allunansa. Kuma abin tambaya shin wane ne dan takararsa tunda ba ya son a sanya wani dan takara, kuma ya manta ba allo ne cin zabe ba, don haka za mu bi doka ba za mu sake sanya allon titi ba don mun san ’yan takararmu na PDP na cikin zukatan mutanen jihar nan, PDP na cikin zukatan Sakkwatawa, muna nan muna jiran doka ta sake ba mu damar sanyawa.
Aminiya: Wasu na ganin tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa ya shigo Jam’iyyar PDP ne domin ya mamaye jam’iyyar me z aka ce kan haka?
Abdullahi MD: Ba gaskiya ba ne, ya shigo PDP ne don ya gyara ta a hada karfi da karfe don kawo sauyi, don cimma burin da yake da shi na ci gaban Sakkwato. Ni shaida ne domin Bafarawa ya yi rantsuwa bai shigo PDP don ruguza ta ba, kuma ya fahimci talakawan Sakkwato na bukatar canji kan haka yake son ya shige masu gaba burinsu ya cika. Yau idan PDP ta kafa Gwamna ba wanda zai kai Bafarawa murna, in faduwa ta yi kuma ba wanda zai kai shi bakin ciki. Maganar mamaya kuwa zancen ’yan adawa ne. Don haka muna bayan Bafarawa kuma koyaushe muna tare dashi a siyasar PDP. Ba tsaran Bafarawa a sanin siyasa, don haka muna tare da shi, don ko cikin gwamnatin yanzu yaransa ne, shi farfesa ne a fannin siyasa.