Har yanzu jita-jita muke ji kan bacewar Manjo Janar Alkali – ’Yan uwansa

Wadansu daga cikin ’yan uwan Manjo Janar Idris Alkali da aka ce ya bace a hanyar Abuja zuwa Jos sun ce su har zuwa yanzu jita-jita kawai suke ji a kan al’amarin dan uwansu tun lokacin da suka daina jin labarinsa bayan ya baro Abuja zai je gonarsa da ke kauyen Jitar a karamar Hukumar […]

Har yanzu jita-jita muke ji kan bacewar Manjo Janar Alkali – ’Yan uwansa
Har yanzu jita-jita muke ji kan bacewar Manjo Janar Alkali – ’Yan uwansa

Wadansu daga cikin ’yan uwan Manjo Janar Idris Alkali da aka ce ya bace a hanyar Abuja zuwa Jos sun ce su har zuwa yanzu jita-jita kawai suke ji a kan al’amarin dan uwansu tun lokacin da suka daina jin labarinsa bayan ya baro Abuja zai je gonarsa da ke kauyen Jitar a karamar Hukumar Bauchi a Jihar Bauchi.

Wata ’yan uwarsa da ke zaune a Bauchi da ta nemi a sakaye sunanta ta ce “Mu dai rokon Allah muke yi ya bayyana mana shi, kuma mahaifiyarsa duk dacewa ta tsufa tana nan a raye kuma tana ta addu’a tana kuma ji a jikinta cewa danta yana da rai.”

Game da ko an sace shi ne ko an kashe shi sai ta ce “Wannan duk Allah ne Ya bar wa kanSa sani, mu dai jita-jita muke ji ta yanar gizo, har yanzu babu wani bayani da muka samu daga hukumomi ko wani sai dai batutuwa da ba su da tabbas muke ta ji muna rokon Allah Ya bayyana mana shi.”

Ta ce hakika sun shiga dimuwa saboda Janar Alkali mutumin kirki ne wanda ba abin da yake ki kamar ya ga an tauye wa na kasa hakkinsa, “Mutum ne mai son mutane mai fara’a mai kulawa da ’yan uwansa da mahaifiyarsa mun yi imani da Allah kuma da ikon Allah, Allah zai kubutar mana da shi,” inji ta.

Game da abubuwan da suke cikin gonar tasa sai ta ce “Gonar tasa akwai dabbobi da tsuntsaye kamar shanu da tumaki da awaki da kaji da kifi da agwagi, yana son gonar kuma yana yawan zuwa.”

Wani babban jami’in ’yan sanda a Jihar Filato ya shaida wa Aminiya cewa “Sun tura mutanensu cikin daji da kududdufai da koguna domin a neme shi kuma har yanzu ana ta kokarin nemansa da niyyar Allah Ya bayyana shi.”

Ya ce “Tun lokacin da muka samu labari da mu da sauran hukumomin tsaro ba mu zauna ba ko kadan, kullum neman hanyar da Allah zai sa mu gan shi muke yi kuma kullum cigiyarsa da bincike muke yi ko Allah zai sa mu gan shi.”

Manjo Janar Mohammed I. Alkali, wanda ya yi ritaya a kwanakin baya a matsayin Babban Jami’in Mulki na Hekwatar Sojin Najeriya majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa ya bace ne a ranar Litinin 3 ga Satumba ranar da yake tafiya Bauchi daga Abuja.

Janar din ya isa Jos da rana inda ya kira gida ya shaida musu. Kuma majiyar ta ce wannan ce tattaunawa ta karshe da wani ya yi da babban jami’in sojan.

“Wayoyinsa sun daina aiki tunda ya kira kira kuma duk kokarin da aka yi don samunsa ya ci tura,” inji majiyar.

Kakakin ’Yan sandan Jihar Filato, Tyopeb Terna, ya ce yayan Janar din Kwamishinan ’Yan sanda Umar F. Idris (mai ritaya) ya kai rahoton lamarin ga ofishin siyya na ’yan sanda da ke Anglo-Jos.

Ya ce tuni suka fara bincike a kan lamarin.

Sannan Shugaban Ma’aikata na Shirin Samar da Zaman Lafiya na OPSH da ke kula da jihohin Filato da Bauchi da wani bangare na Kaduna Birgediya Janar Muhammed Bello, ya ce suna sane da lamarin. Y ace tuni sun samu umarni daga Hedkwatar Soji kan su binciki lamarin inda ya ce sun fara aikinsu a yankunan da suke da iko.

Birgediya Bello ya ce ba su tuntubi iyalansa ba ne saboda batu ne na hedkwata, kuma za su yi bakin kokarinsu wajen sauke nauyin da aka dora musu.

Majiyarmu ta ce Janar Alkali yana tafiya ce a wata mota kirar Toyota Corola mai Lamba MUN 670 AA.