Har yanzu Kano ba ta cika alkawarin gidajen da ta yi wa ’yan kwallon Golden Eaglets ba
’Yan kwallon Eaglest sun koka a kan rashin cika alkawarin da Gwamnatin Kano ta yi musuKimanin shekara biyu kenan da gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Injiniya Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ta yi wa ’yan kwallon Golden Eaglests da suka lashe gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) da ya gudana a […]
’Yan kwallon Eaglest sun koka a kan rashin cika alkawarin da Gwamnatin Kano ta yi musu
Kimanin shekara biyu kenan da gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Injiniya Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ta yi wa ’yan kwallon Golden Eaglests da suka lashe gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) da ya gudana a Dubai alkawarin ba su gidaje amma har yanzu abin bai tabbata ba.
Ita dai gwamnatin Kano ta yi wa ’yan kwallon Eaglets da suka fito daga Jihar watau Musa Muhammed da Zaharadeen Bello alkawarin ba kowannensu gidaje ne bayan sun samu nasarar lashe kofin a Dubai a shekarar 2013 amma kawo yanzu shiru kake ji kamar an shuka dusa.
Musa Muhammed, shi ne kyaftin din kungiyar ta U-17 da suka samu nasarar lashe kofin a shekarar 2013 yayin da Zaharadeen kuma yake daya daga cikin ’yan kwallon da suka samu nasarar lashe kofin, kuma su biyun ’yan asalin Jihar Kano ne bayan sun koma gida ne jim kadan da lashe kofin sai Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi musu alkawarin ba kowannensu gidaje.
“Na ziyarci Hukumar zuba jari da kula da kadarori na Jihar Kano sau shurin masaki game da batun gidajen namu amma kullum sai su ce min har yanzu babu labari. Na gana da Manajin Daraktan Kamfanin Dauda Sheshe amma abin ya faskara.”
“Abin bakin ciki shi ne yadda muka kasa ganawa da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso a kan wannan batu amma muna fata da zarar ya karanta labarin a jarida zai yi wani abu a kai”.
Sai dai wata majiya ta kyankyasawa manema labarai cewa akwai yiwuwar wani kamfani da ya fito daga Sin mai suna Chinese Group ne Gwamnatin Kano ta sayarwa gidajen da ke rukunin Amana Estate kuma ciki har da gidajen da aka yi wa ’yan kwallon alkawari.