Har yanzu kasuwancin soson gargajiya bai mutu ba – Usman Maisoso
Soso wani nau’i ne na tsiro da yake yin yado a dazukan Kurmi da ake nado shi a shanya ya bushe sannan a sarrafa shi zuwa soson wanka da wanke-wanke. Soson gargajiya ba ya cikin nau’in ciyayi ko bishiyoyi, yana yin yado ne a cikin daji. Kuma ana samunsa a kowane lokaci na rani da […]
Soso wani nau’i ne na tsiro da yake yin yado a dazukan Kurmi da ake nado shi a shanya ya bushe sannan a sarrafa shi zuwa soson wanka da wanke-wanke. Soson gargajiya ba ya cikin nau’in ciyayi ko bishiyoyi, yana yin yado ne a cikin daji. Kuma ana samunsa a kowane lokaci na rani da damina.
Alhaji Umaru Muhammed wanda ya shafe shekara 40 yana harkar saye da sayar da soso a garin Omi Adio a Jihar Oyo ne ya yi wa Aminiya wannan bayani.
Ya ce, “An fara harkar nemo soso da sarrafa shi ne kaka da kakanni kuma ana samun irin wannan soso mai inganci a cikin dazukan Kurmi. Leburori ne suke shiga daji domin samo shi suna sayarwa ga dillalai su kuma su sayar ga masu sarrafawa. Akwai Soson Gora da ake kawowa daga Arewa, amma bai kai ingancin irin wannan ba.”
Da yake amsa wata tambaya, Alhaji Umaru Muhammed cewa ya yi “Kashi 100 na masu shiga daji da dillalai da masu sarrafa soson duka ’yan Arewa ne. A gaskiya bullowar sabon soson zamani da ake yin sa da roba ko zare ya rage yawan masu sayen soson gargajiya amma bai kashe mana kasuwar kwata-kwata ba,” inji shi.
Wani Dattijo mai suna Usman Maisoso, wanda ya shafe shekara 30 yana sarrafa soson gargajiya a Unguwar Sabo, Ibadan, ya shaida wa Aminiya cewa “Ba na cikin masu shiga dajin Kurmi domin nemo danyen soso, amma ina saya daga hannun mutanenmu da suke kawo mana.”
Dattijo Usman ya ce, “Ban taba yin wata sana’a ko aiki a tsawon wannan lokaci ba. Na dogara da sana’ar sarrafa soso da sayarwa ne wajen biyan bukatuna da iyalina a tsawon shekara 30 da suka wuce. Batun fitowar soson roba kuwa, ai hanyar jirgi daban ta mota daban, domin kamar yadda muka saba har yanzu muna sayar da soson gargajiya ga mabukata. Bullowar soson zamani bai kashe mana kasuwa ba.”