Har yanzu muna bin Shinkafi bashin kudin kamfen na 2007 – Gwamna Yari
Tun lokacin da ake tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi ya hau kujerar Gwamna a shekara ta 2007, muka ciyo bashin Naira miliyan 450 a wajen wani aminina don gudanar da yakin neman zabe, amma har yanzu ba a biya shi ba. Wannan kalamin ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji […]
Tun lokacin da ake tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi ya hau kujerar Gwamna a shekara ta 2007, muka ciyo bashin Naira miliyan 450 a wajen wani aminina don gudanar da yakin neman zabe, amma har yanzu ba a biya shi ba.
Wannan kalamin ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar, lokacin da yake jawabi a wajen taron yakin neman zabensa a karo na biyu a garin Gusau babban birnin jihar.
Gwamna Yari ya ce “Lokacin da tsohon Gwamnan Mamuda Shinkafi zai yi takara, Sanata Sani Yarima ya nemi mu bada rance ga Mamuda amma ba a samu ba, sai ni na roki wani aminina ya bada rancen Naira miliyan 450 a wancan lokaci, kuma har yanzu ba a maida masa kudinsa ba.”
Gwamna Yari ya ce aminin nasa ya gudanar da kwangila da kungiyar NULGE na sayo babura da aka ce za su biya cikin wata takwas, sai aka shirya da Gwamna Yarima aka biya shi, bayan an biya sai suka karbi rancen Naira miliyan 450 wadda har yanzu ba a biya shi ba.
Ya ce akwai shaidu kan haka, ciki har da Musa Mallaha, sai dai a cewarsa tsohon Gwamnan ya ce tunda kudin na Yariman Bakura ne da Abdul’aziz Yari ba zai biya ba.
Gwamna Yari ya ce baya haka akwai Naira biliyan 32 da gwamnatin Mamuda ta yi wa al’ummar Jihar Zamfara almundahana, ciki har da miliyan 69 da digo 9 da tsohon Gwamnan ya ce zai yi amfani da sune wajen gina kananan sakandire, a wasu kananan hukumomi.
Gwamna Yari ya kara da cewa cikin manyan ayyuka 30 da tsohon Gwamnan yake cewa ya gudanar babu wanda aka yi kashi 60 cikin 100 na aikin.
Ya kawo misali da Gadar Karakai da tsohon gwamnan ya ce ya yi, inda Gwamna Yari ya ce hanyar ma gaba daya shi ya yi ta, kuma ban da Gadar Karakai akwai wasu hudu da ya yi su ciki har da ta garin Gama Giwa.
Gwamna Yari ya ce, ya ki bincikar Mamuda ne saboda kada siyasa ta shigo ciki. Amma idan ya fadi zabe ya koma tsohon dan takarar Gwamna, za su gayyace shi don ya zo ya yi wa al’ummar Jihar Zamfara bayanin yadda ya yi da dukiyarsu.