Har yanzu muna fama da matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari – Dan Majalisa

Honorabul Salisu Isa shi ne wakilin mazabar Magajin Gari da ke Birnin Gwari a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, a tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana halin da ake ciki a yankin Birnin Gwari mai fama da rashin tsaro inda ya ce har yanzu matsalar rashin tsaro na damun jama’arsu:    Wani hali al’ummar mazabarka ta Birnin […]

Har yanzu muna fama da matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari – Dan Majalisa

Honorabul Salisu Isa shi ne wakilin mazabar Magajin Gari da ke Birnin Gwari a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, a tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana halin da ake ciki a yankin Birnin Gwari mai fama da rashin tsaro inda ya ce har yanzu matsalar rashin tsaro na damun jama’arsu: 

 

Wani hali al’ummar mazabarka ta Birnin Gwari ke ciki a yanzu musamman game da rashin tsaro?

Muna godiya ga Allah muna kuma ci gaba da rokon Allah Ya kawo mana sauki domin a yanzu babu shakka gwamnati tana iya kokarinta don kare rayuka da dukiyoyin mutanenwannan yanki. Amma kamar abin da muka sani ne yana faruwa a yankin Maiduguri to sai mu dauki abin da ke faruwa a yankin Birnin Gwari kamar waccan duk da cewa bai kai waccan ba. Domin muna da wani daji ne mai girman gaske da ’yan ta’addan ke shiga suna boyewa, tsakaninsu da jami’an tsaro sai boye-boye idan an kai musu farmaki nan sai su koma can. 

Mutane suna jin dadin matakan da ake dauka kwarai da gaske amma har yanzu matsalar na nan ba a kawar da da ita gaba daya ba, amma ana ci gaba da samun sauki idan aka yi la’akari da inda aka fito.

Da wannan nake kira ga gwamnati cewa muna neman dauki har yanzu, mun gode mun kuma yaba da kokarin da ake yi amma muna neman a kara taimaka jami’an tsaro da suke aiki a yankin da kayan aiki domin magance batagarin. Labaran da muke samu wadannan dazuzzuka ba su da kyau domin akwai bayanan da suke cewa wadansu mutane da ake ganin ’yan Boko Haram ne suke baro bangarorinsu suna tarewa a dajin kuma suna da makamai don haka muke kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jiha a kara kaimi domin kare al’ummarmu da wadanda ke bi ta hanyar da ta ratsa Birnin Gwari, wadda ta hada Arewa da Kudu sai mutum ya taso daga Legas amma da zarar ya iso Birnin Gwari sai hankalinsa ya tashi matuka. Ina da yakinin idan aka yi maganin matsalar tsaro a yankin namu babu shakka ba mutanen Jihar Kaduna kawai ba duk Najeriya za su amfana.

 

Kwanan nan ne wadansu ’yan ta’adda suka kai hari a wasu kauyuka, wane hali mutanen da suka ji raunuka ke ciki a yanzu?

Babu shakka ta’addancin ya shafi mutane da yawa domin farmakin da jami’an tsaro ke kai musu ya sa ana kashe su da yawa da fatattakarsu, wannan ya sa su ma sai su sadado su far wa kauye ta hanyar kashe mutane a matsayin ramuwar gayya. Wadanda Allah Ya dauki rayukansu muna yi musu addu’ar Allah Ya jikansu. kauyuka hudu ne abin ya shafa kuma sun kashe jama’a sun ji wa wadansu raunuka. A gwamnatance muna kokarin ganin cewa idan irin wannan abu ya faro mun samar da magani ga wadanda suka ji ciwo. Wadanda kuma suka rasu za mu je a yi jana’iza da mu sannan idan akwai dan tallafi sai a yi wa iyalansu. Muna kuma kira ga gwamnati ta shigo wajen tallafa wa wadannan mutane da abin ya shafa. 

 

Ko kun gamsu da tsaro da ake bayarwa a hanyar yanzu?

Za mu ce mun gamsu amma ba muna nufin ba a bari ba, mun gamsu domin daga Kaduna zuwa Birnin Gwari idan ka dubi inda aka fito a baya babu shakka an samu ci gaba, domin cikin kashi 80 cikin 100 na matsalar da ke faruwa kan hanya an yi maganinta. Muna rokon a ci gaba da yin amfani da dabarun da ake amfani da su, a kuma kara daukar matakan da suka fi wadanda ake amfani da su a yanzu ta yadda za a magance yawan zuwan ’yan ta’addan suna tare hanya su sace mutane ko fashi.

Sannan daga bangaren Funtuwa zuwa Birnin Gwari zan iya cewa bai wuce kashi 50 cikin 100 ba gaskiya, domin dajin ya fi yawa a wancan bangaren kuma kauyuku sun fi yawa sannan hanyar ta lalace sosai motoci ba su iya tafiya da sauri kamar na nan Kaduna. Ko hanyar ta kaduna zuwa Birnin Gwari tana bukatar gyara don haka ina kira ga Gwamnatin Tarayya cewa gyaran da aka faro a yankin Labe zuwa Buruku aka tsaya a zo a ci gaba zuwa Birnin Gwari. Domin idan motoci na wucewa da sauri akan samu saukin tsare su a kan hanya. Amma hanyar Funtuwa zuwa Birnin Gwari ta lalace ta wuce misali kuma dajin da muke da shi mafi yawansa a wancan bangare yake, don haka har yanzu ana fashi sai dai ba kamar da ba. 

 

Ko za ka iya fada mana nasarori da al’ummarka suka samu a hawanka wannan kujera? 

Nasarori mun same su da yawa musamman idan muka kalli shekara biyu da rabi kawai da muka yi a kan mulki da shekara 16 da aka yi a baya. Duk da matsalar kudi da ake fama da ita a gwamnatance idan aka sake wasu shekara biyu da rabi nan gaba to, aikin da za mu yi a shekara biyar sai ya ninka aikinsu na shekara 16. Misali duk wanda yake zaune a garin Birnin Gwari idan ya shiga cikin gari ya ga aikin da ake yi zai ga cewa ba a taba yin irinsu ba tun da aka dawa mulkin dimokuradiyya. Domin hanyoyi ne masu inganci ba na jeka na yi ka ba. Sannan akwai bangarori biyu na yamma inda Gwamnatin Tarayya na can na ta kokari ta yadda za a samu saukin kai kayan abinci kasuwa. Akwai ayyuka da gwamnatin jiha ta bayar ana nan ana ta aiki, kuma akwai asibitoci da makarantu da ake ta gyarawa da sauran abubuwan ci gaba. 

Don haka idan ci gaba ake magana zan ce al’ummar Birnin Gwari sun dace da zaben Jam’iyyar APC da suka yi a karkashin Shugaba Muhammaduu Buhari da Gwamna Nasir El-Rufa’i da mu ’yan Majalisar Jihar Kaduna. 

 

Yaya dangarta take tsakanin ku majalisa da bangaren zartaswa?

Dangartakar tana da kyau kwarai da gaske wannan ya sa wadansu ke yi mana kallon ’yan amshin shata, saboda wai ba su ga muna fada da Gwamna ba. Wannan yana faruwa ne idan ba a fahimci abin da mutum ke yi ba. Amma idan mutum ya zaunar da kai ya fahimtar da kai abin da yake har ka gamsu ba son ransa ba ne, yana yi ne don mutane su amfana kuma mutanen nan ne suka zabe mu, kuma mun yi alkawarin rike amana wanda shi ne kirarin jam’iyyarmu ta APC Canji, Canji, amana. 

Yana iya yiwuwa gyaran da ake yi wanda ba ya wajen tunaninsa bai yi nisa ba ba zai gano gyaran ba a lokacin. Kamata ya yi mutum ya fito kai-tsaye ya ce ga abin da ake yi da ba na ci gaba ba a jiha, a majalisa akwai kwamitin da ke karbar korafi amma har yanzu babu wanda ya kai korafin da suka gamsar da majalisa a kan abin da gwamnati ke yi wanda ba daidai ba. kofa a bude take duk wanda ke da korafi yana iya kai wa majalisa idan ya gamsar da ita za ta jawo hankalin bangaren zartarwa domin a gyara.

 

Mene ne sakonka ga al’ummar Birnin Gwari?

Kamar yadda na fada mutanen Birnin Gwari dai sun ga aiki a kasa a bangaren ci gaba illa maganar tsaron nan da muke cewa ita ce babbar matsalar da ke damun mu, kuma babu shakka ba za mu daina magana a kai ba har sai lokacin da mutumin Birnin Gwari zai fito ya gudanar da rayuwarsa cikin jin dadi kamar kowane dan yankin jihar. Kuma muna kira ga jama’ar yankin su ci gaba da bai wa wannan gwamnati goyon baya wanda idan suka yi haka za a samu ci gaba fiye da na baya. Sannan mutanen Jihar Kaduna da Najeriya su tuna da akwai inda mutum ba ya son zuwa saboda tsoron bam, a masallaci tsoro, a coci tsoro, har an yi lokacin da ake bi gida-gida ana cin zarafin mutane da sunan magance tsaro. Wannan ya sa muke kira ga jama’a su ci gaba da yi wa wannan gwamnati addu’a da goyon baya domin ta ci gaba da inganta rayuwarsu.