Har yanzu mutanen Jos suna cikin mawuyacin hali – Shehu Musalla
Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Jasawa na kasa Alhaji Shehu Musalla ya bayyana cewa har yanzu al’ummar Jos suna cikin mawuyacin hali, sakamakon yadda aka yi watsi da su wajen samar masu da abubuwan more rayuwa kamar hanyoyi da ruwan sha da asibititoci. Alhaji Shehu Musalla ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi […]
Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Jasawa na kasa Alhaji Shehu Musalla ya bayyana cewa har yanzu al’ummar Jos suna cikin mawuyacin hali, sakamakon yadda aka yi watsi da su wajen samar masu da abubuwan more rayuwa kamar hanyoyi da ruwan sha da asibititoci.
Alhaji Shehu Musalla ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron tunawa da daruruwan al’ummar Jos da aka kashe a lokacin rikicin zaben karamar hukumar Jos ta Arewa na ranar 28 ga watan Nuwamban shekara ta 2008 a ranar Talatar nan.
Har’ila yau ya ce tun da aka yi wannan rikici na ranar 28 ga watan na Nuwamba na shekara ta 2008, da ya yi sanadin asarar daruruwan al’ummar Jos tare da dukiyoyinsu har ya zuwa wannan lokaci, ba a hukunta kowa ba, ‘’Muna son a hukumta wadanda suke da hanu a wannan rikici, domin ya zamo darasi ga sauran jama’a masu hali irin wannan. Kuma muna son gwamnati ta biya diyya ga wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan rikici’’.
Daga nan ya yaba da yadda jam’iyyu suka gudanar da zaben tsayar da ‘yan takarar zaben shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa, wanda za a gudanar a ranar 17 ga watan biyu na sabuwar shekara mai zuwa.
Ya yi kira ga gwamnan Filato Simon Lalong ya cika alkawarin da ya yi, na yin gaskiya da adalci a zaben kananan hukumomin jihar da za a yi musamman a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban taron Alhaji Ibrahim Sale Hassan ya bayyana cewa a duk rikice rikicen da aka yi a jihar Filato, ba a taba rikicin da aka rasa rayukan mutane kamar wannan rikici na ranar 28 ga watan Satumba na shekarar 2008 ba.
Har’ila yau ya ce a duk lokacin da suka shirya taron, suna tattauna hanyoyin da za su bi su gyara dangartakarsu da abokan zamanmu, domin a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali da cigaba.
Shima a takardar da ya gabatar a wajen taron Alhaji Sani Sulieman Maigoro ya bayyana cewa matsalolin da suka hana zaman lafiya tsakanin Jasawa da abokan zamansu. Sune batun dan kasa da bako da gazawar gwamnati wajen samar da abubuwan kyautata rayuwa kamar hanyoyin mota da ruwan sha da makarantu da asibitoci da dai sauransu a garin Jos.