Har yanzu Najeriya na buƙatar shugabanni nagari – Sheikh Gumi

Sheikh Gumi ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ta addabi wasu yankunan ƙasar nan.

Har yanzu Najeriya na buƙatar shugabanni nagari – Sheikh Gumi

Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce har yanzu Najeriya na neman shugabanni nagari da za su fifita jin daɗin al’umma maimakon mayar da hankali kan wajen tara wa kansu dukiya.

Ya bayyana hakan ne yayin bikin karramawa da ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Makarantar Firamare ta Sultan Bello (SUBOPA), ta shirya domin girmama wasu mambobinta biyu – Manjo Janar Abdulmalik Jibrin (mai ritaya) da Birgediya Janar Abdulkadir Gumi (mai ritaya), bisa sababbin muƙaman da suka samu a gwamnati.

An naɗa Manjo Janar Jibrin a matsayin Sakatare na Hukumar Kula da Tsaro na Fararen Hula, yayin da aka naɗa Birgediya Janar Gumi a matsayin Shugaban Kwamitin Tallafin Tsaro na Jihar Zamfara.

Sheikh Gumi ya yaba wa Manjo Janar Jibrin bisa aiki tuƙuru da ɗa’a, inda ya ce har yanzu Najeriya na buƙatar shugabanni kamar shi waɗanda ke da gaskiya, horo mai kyau, da kuma kishin al’umma.

“Wannan ya faru ne saboda Najeriya na matuƙar buƙatar shugabanni nagari da za su jagoranci ƙasar nan.

“Muna buƙatar mutane masu tarbiyya da ladabi waɗanda ke da niyyar taimaka wa wasu, ba kawai kansu ba.

“Mutanen da ke da kyawawan halaye da ɗabi’u su ne ya kamata ake bai wa muƙaman shugabanci a ƙasar nan,” in ji shi.

Ya kuma soki shugabannin yanzu, inda ya ce: “Ba irin shugabannin da muke da yanzu a ƙasar nan ba, waɗanda kawai ke tunanin kansu da iyalansu.”

Da yake magana kan matsalolin da Najeriya ke fuskanta, Sheikh Gumi ya nuna damuwarsa kan tasirin matsalar tsaro, musamman a jihohin da suka haɗa da Zamfara, inda matsalar ta janyo koma baya a ɓangaren ilimi tare da haifar da rashin zaman lafiya a wasu yankuna.

Ya jinjina wa Gwamnatin Jihar Zamfara bisa bai wa Birgediya Janar Gumi muƙami, wanda ya ce zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro.

A nasa jawabin, Shugaban SUBOPA, Mohammad Babayo Hassan, ya ce naɗin da aka yi wa mambobinsu ba kawai nasararsu ba ce, wata alama ce ta ɗabi’u da ƙwazon da suka koya daga makarantarsu.

Da yake magana a madadin waɗanda aka karrama, Manjo Janar Abdulmalik Jibrin ya keɓe lambar yabon ba ta shi ce shi kaɗai ba, face ta dukkan mambobin ƙungiyar ne.