…Har yanzu ni ne halastaccen Shugaban Zimbabwe Mugabe

Shugaba Mugabe ya ce shi ne halartaccen Shugaban kasar Zimbabwe, bayan ya ki amincewa da sulhun da wani malami Cocin Katolica ya jagoranta. Malamin Cocin, Fidelis Mukonori, wanda shi ne ke jagorancin sulhu tsakanin Mugabe da rundunar sojin kasar, ya shiga tsakani ne domin a samu yadda za a tattauna har Mugabe ya sauka cikin […]

…Har yanzu ni ne halastaccen Shugaban Zimbabwe Mugabe

Shugaba Mugabe ya ce shi ne halartaccen Shugaban kasar Zimbabwe, bayan ya ki amincewa da sulhun da wani malami Cocin Katolica ya jagoranta.

Malamin Cocin, Fidelis Mukonori, wanda shi ne ke jagorancin sulhu tsakanin Mugabe da rundunar sojin kasar, ya shiga tsakani ne domin a samu yadda za a tattauna har Mugabe ya sauka cikin mutunci, kamar yadda Reuters ta ruwaito.

Majiyar da Reuter ta samo bai ba da cikakken bayani ba a kan tattaunawar da ake ciki, amma dai da alamu ana so ne a rabu lafiya da Shugaba Mugabe wanda shi ne Shugaban kasar tun lokacin da ta samu ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.