Har yanzu ni ne halastaccen Shugaban Zimbabwe-Robert Mugabe
Shugaba Mugabe ya ce shi ne halartaccen Shugaban Qasar Zimbabwe, bayan ya qi amincewa da sulhun da wani malami Cocin Katolica ya jagoranta. Malamin Cocin, Fidelis Mukonori, wanda shi ne ke jagorancin sulhu tsakanin Mugabe da rundunar sojin qasar, ya shiga tsakani ne domin a samu yadda za a tattauna har Mugabe ya sauka cikin […]

Shugaba Mugabe ya ce shi ne halartaccen Shugaban Qasar Zimbabwe, bayan ya qi amincewa da sulhun da wani malami Cocin Katolica ya jagoranta.
Malamin Cocin, Fidelis Mukonori, wanda shi ne ke jagorancin sulhu tsakanin Mugabe da rundunar sojin qasar, ya shiga tsakani ne domin a samu yadda za a tattauna har Mugabe ya sauka cikin mutunci, kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Majiyar da Reuter ta samo bai bada cikakken bayani ba a kan tattaunawar da ake ciki, amma dai da alamu ana so ne a rabu lafiya ta Shugaba Mugabe wanda shi ne Shugaban Qasar tun lokacin da ta samu ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.