Har yanzu PDP mushen gizaka ce
Talakawan kasar nan sun dade suna jiran labarin darewar jam’iyyar PDP, domin kuwa tun daga lokacin da suka ji gangarta ta faye zaki bayan zaben 2011, suka san ta kusa fashewa. Dangane da haka ana iya cewa bijirewar da wasu shugabanni da manyan ‘ya’yan jam’iyyar PDP da kuma wasu gwamnoninta guda bakwai suka yi a […]
Talakawan kasar nan sun dade suna jiran labarin darewar jam’iyyar PDP, domin kuwa tun daga lokacin da suka ji gangarta ta faye zaki bayan zaben 2011, suka san ta kusa fashewa. Dangane da haka ana iya cewa bijirewar da wasu shugabanni da manyan ‘ya’yan jam’iyyar PDP da kuma wasu gwamnoninta guda bakwai suka yi a Abuja, a makon jiya, bai ba kowa mamaki ba domin kuwa wanan ba sabon abu ba ne, ganin cewa duk abin da aka gani ya faru a siyasar Najeriya an taba yin irinsa. Tun daga lokacin da kungiyar Gwamnonin Najeriya ta shiga matsalar da ta kai tsagewarta gida biyu, saboda biye wa son zukatan manyan shugabanninta, wadanda suka guje wa gaskiya, suka kuma sayar da lafiya, suka sayo cuta, sai matsalolin da suka dade da addabar jam’iyyar PDP suke ta kara kamari.
Dalili ke nan da ya sa matsaloli suka rika sauko wa jam’iyyar tamkar ruwan damina a watan marka-marka, har ma ta kai ba ta iya sarrafa ragamar mulkin gwamnatinta yadda ya kamata, domin kasancewar shugabanninta lusaran da ba su iya bambance karya da gaskiya. Rikice-riken da suka yi katutu a cikinta, aka kuma kasa samun wadanda za su yayyafa musu ruwa, sai dai masu dada ingiza itatuwan wutar da ke konata, sun ci gaba da rarraba akawunan shugabanni da mabiyansu, sa’annan kuma daga cikinsu ba wani mai yin fatan alheri sai mugun alkaba’in da zai iya kai jam’iyyarsu kasa.
Daga cikinsu akwai wadanda suka takarkare wajen yin addu’a don dorewar barakar da ta wanzu a halin yanzu, wacce ake jin cewa za ta iya jawo wargajewar jam’iyyar cikin hanzari, tun da dai ba wasu shugabannin da za su tsawata, wadanda kuma za su sasanta sun gamu da batar basira. Wadannan al’amara sun samo asali ne daga mugun zaren da aka saka zanin da aka kunshe jam’iyyar da shi tun tana ‘yar jaririya, da kuma wannan zaren ne aka saka majayin da aka goya ta. To akwai wanda zai yi mamaki a yanzu idan wannan jam’iyar ta haifi ‘ya’yan da za su dinga wanke mata hannu akai, suna mata hawan kawara yadda suka ga dama? Ai barewa ba za ta yi gudu ba sa’annan diyarta ta yi sassarfa. Shi ya sa wasu ‘ya’yan jam’iyyar na asali, wadanda suka yi dawainiya da hakilo wajen kafa wannan jam’iyar, aka kuma nuna musu iyakansu, suka dawo daga rakiyarta. To amma bisa ga dukkan alamu wannan al’amarin da ya tayar da zaune tsaye a cikin jam’iyyar PDP har ya yi sanadiyyar karan-tsayen da ‘ya’yanta suka yi mata zai kara tabarbarewa ne, kuma kamar yadda masu magana ke cewa, “idan tururuwa ta tashi lalacewa sai ta yi fika-fikai.”
Duk kokarin da aka yi don kashe wutar da ke dumama PDP tun tana ‘yar karama ta ci tura, an kuma yi sake dan zaki ya girma, gwamnonin jam’iyyar tun suna nuna wa uwarsu yatsa, har ta kai ga tadiye ta kasa, a bainal-jama’a. Ba wani abu ba ne kuwa ke haddasa tsuguni-tashi cikin jam’iyyar PDP ba illa batun takara, da wasu ‘yan tsirarun cikin jam’iyyar, wadanda suka yi amfani da addini da kabilanci don dora Goodluck Jonathan bisa karaga, suke ke so ya yi, da kuma yadda shi da kansa ya daurewa Alhaji Bamanga Tukur gindi a shugabancin jam’iyyar saboda ta kansa ne zai bi ya samu biyan bukatar sake tsayawa zabe. Yanzu wadancan fandararrun ‘ya’yan jam’iyya sun gicciya wasu ka’idoji don sasantawa, kuma bisa ga dukkan alamu loma ce suka yanko wacce za ta fi karfin bakin shugabannin PDP, kuma da wuya su amince da su.
Idan ba mahaukacin kare ne ya ciji Jonathan ba zai yarda ya ki yin takara, asirinsa ya tonu a banza? Haka nan kuma zai yi kirari ne, ya daba wa cikinsa zabgegegiyar wuka idan ya amince da korar Bamanga daga shugabancin jam’iyya? Idan suna da gaskiya me zai sa su razana da hukumar EFCC, har su nemi a tsawata mata ta daina yi masu barazana?
Wannan rikici dai ba sabon abu ba ne ga jam’iyyar, tsohon shugabanta na farko, Cif Solomon Lar ya taba ballewa tare da wasu makarrabansa a shekarar 2006, suka kafa sakatariyar bangarensu a Abuja, amma daga karshe Olusegun Obasanjo ya kashe wannan wutar, jam’iyyar ta dinke dif. A yanzu ma haka na iya faruwa, domin wasu na cewa da gangan ne aka tsiri wannan makircin don a share fagen zarcewar Jonathan bisa mulki. To koma dai mene ne tura ta kai bango, an ga shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar PDP a rana, kuma kowane bangare cewa yake tusa ta karewa bodari.