Har Yanzu Shekarau ne dan takarar NNPP a Kano ta Tsakiya —INEC

INEC ta ce lokaci ya kure ne maye gurbin Shekarau a matsayin dan takarar Sanata

Har Yanzu Shekarau ne dan takarar NNPP a Kano ta Tsakiya —INEC

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce har yanzu tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, shi ne dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar NNPP.

Tun ranar 29 ga watan Agusta, 2022, Shekarau ya sauya sheka daga NNPP zuwa Jam’iyyar PDP, amma INEC ta fitar da sunansa a matsayin dan takarar jam’iyyar.

A ranar Talata, 20 ga watan Satumba, 2022 ne hukumar ta fitar da jerin karshe na sunayen ’yan takarar shugaban kasa da Majalisar Dokoki ta Tarayya a babban zaben da za a gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Ganin sunan Shekarau a matsayin dan takarar Kano ta Tsakiya a NNPP — alhali tun lokacin sauya shekararsa ya sanar da jam’iyyar da INEC cewa ya janye daga takararsa  — ya janyo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa.

Aminiya ta tuntubi INEC kan wannan lamari, inda Kwamishina na Kasa kan Yada Labarai da Wayar da Kai na hukumar, Festus Okoye, ya tababtar mata cewa har yanzu tsohon gwamnan shi ne dan takarar NNPP.

Ya ce, “Jadawalin zaben da muka fitar ranar 26 ga watan Fabrairu, 20202 ya sanya 15 ga watan Yuli, 2022, a matsayin ranar karshe ta janyewa daga takara ko sauya dan takarar Majalisar Dokoki ta Tarayya.

“Shi kuma tsohon gwamnan ba tashi janye takarar tasa ba sai ranar 26 ga watan Agusta, 2022.

“Hakan na nufin har yanzu shi ne dan takarar NNPP kuma sunansa ne zai fito a takardar kada kuri’a a matsayin mai neman kujerar a jam’iyyar.

“Bayan ranar 15 ga Yuli, 2022, ba za a iya asuya dan takara ba, sai idan mutuwa  ya yi ko kuma kotu ta bayar da umarni, saboda kofar yin haka ta riga ta rufe,” in ji shi.

Za mu dauki matakin da ya dace —NNPP 

Da yake tsokaci kan lamarin, kakakin NNPP na Jihar Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya ce jam’iyyar ba ta yi mamakin ganin sunan tsohon gwamnan a matsayin dan takararta ba, amma ta riga ta fara yin abin da ya dace domin shawo kan lamarin.

Rogo ya ce dokar zabe ta riga ta tsara matakan da za a bi domin sauya dan takara a irin wannan yanayi, tuni kuma jam’iyyar ta fara aiwatarwa domin sauya sunan tsohon gwamnan.

Ya bayyana cewa bayan Shekarau ya janye don kashin kansa, jam’iyyar ta gudanar da sabon zaben dan takara kafin karewar wa’adin da dokar zabe ta bayar.

“Komai mun yi shi ne a kan lokaci a bisa tsarin da ya dace, saboda haka mun riga mun tattara hujjojinmu, za mu je kotu kuma mun tabbata kotu za ta umarci INEC ta maye gurbin tsohon takarar da sunan sabon da muka gabatar.

“Yanzu kawai ranar sauraron karar muke jira,” in ji shi, amma ya ki yin karin bayani kan sauran abubuwan da ke cikin karar da suka shigar.

Da kamar wuya —Lauya

Game da halascin yin hakan da INEC ta yi, tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) Aliyu Nassarawa, ya ce Dokar Zabe ta 2022 ta nuna da idan aka gabatar da sunan dan takarar, to maye gurbinsa abu ne mai wuya. 

Ya ce idan NNPP ta bi jadawalin zaben da INEC ta fitar yadda ya kamata,  to tana da kwakkwaran hujja a gaban kotu da za ta iya samun biyan bukata.

Amma, “A wurin INEC, sunayen da take da su a kundin bayananta kadai za ta fitar.”

“Kotu ce za ta yi alkalanci (game da makomar jam’iyyar),” a cewarsa.

Shi ma tsohon Shugaban NBA na Jihar Kano, Abdulrazaq Aikawa, ya ce yana da yakini cewa Jam’iyyar NNPP za ta yi duk abin da ya dace domin ganin INEC ta gyara “kuskuren”.

Daga Sagir Kano Saleh Ismail Mudashir (Abuja) & Clement A. Oloyede (Kano)