Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba
Wata majiya ta ce marigayin ya rasu sakamakon ciwon siga da hawan jini.
Matar marigayi Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya), Hajiya Amina Abubakar, har yanzu tana hannun ’yan bindigar da suka sace su a Jihar Katsina.
An sace ta tare da mijinta a ranar 30 ga watan Mayu, 2026, lokacin da ’yan bindiga suka kai wa motarsu hari a kan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli a Ƙaramar Hukumar Matazu.
- An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina
- Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa
A wani bidiyo da aka ɗora a intanet, an ga yadda ’yan bindigar da suka sace su suka tilasta musu yin magana tare da neman ɗauki.
A cikin bidiyon, matar ta yi kira ga gwamnatin Jihar Katsina da ta cika buƙatun ’yan bindigar, ciki har da sakin wasu mut uku da aka kama musu da kuma dawo da shanu da aka ƙwace a hannunsu.
Sai dai daga baya gwamnatin Katsina ta sanar cewa Janar Rabe ya rasu ne sakamakon ciwon siga da hawan jini yayin da yake hannun ’yan bindiga.
Jami’an tsaro sun ce ana ci gaba da ƙoƙarin ceto matarsa, amma ba su bayyana cikakken bayani kan hakan ba.
A gefe guda, wani shugaban ’yan bindiga cikin saƙon murya ya bayyana cewa ya dakatar da shirin sakin matar saboda yawan jami’an tsaro da aka baza a yankin.
Ya kuma buƙaci a saki wasu daga cikin mutanensa da kuma mayar musu da shanun da aka ƙwace, yana cewa hakan na iya taimakawa wajen kawo zaman lafiya a yankin.
Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaro na ci gaba da farautar maharan da suka sace marigayin tare da matarsa.